TARON NGOS AKAN MATSALOLIN KULA DA LAFIYAR MASU JUNA BIYU A LONDON.
September 1, 2004Matsaloli na kiwon lafiya ta fannin haihuwa a nahiyar Afrika na dada tabarbarewa,a cewar wani sabon rahoto dangane da matsaloli dake tattare da haihuwa da daukan ciki.
Wannan bayani na kunshe cikin wani rahoto na musamman da aka gabatar a wajen bukin bude taron yini uku a birnin London,dangane da inda aka dosa kann harkokin kiwon lafiya ta fannin haihuwa,taron da kungiyoyi masu zaman kansu suka shirya.
Kungiyoyin kayyade iyali ta PAI da mai kulawa da Iyalai ta FCI da hukumar international Planned parenthood federation,sun gano cewa kasashe 23 sun samu cigaba ta fannin ingasnta kiwon lafiya wajen haihuwa,kamar yadda aka zartar a taron kasa da kasa kann batun a shekarata 1994,sai dai kasashe 17 basu cimma wani tudun dafawa ba,face koma baya.
Sama da wakilai 700 daga kasashe 109 ne ke halartan wannan taro domin cimma burin da aka sanya gaba na cimma wannan buri nan da shekarata 2015,kamar yadda hukumar ta ICPD ta bada waadi.Ana dai laakari da batutuwa da suka hadar da yawan yara mata dake shiga makarantun sakandare,yaya kwatancin yawansu yake da takwarorinsu maza,adadin jamian kula da lafiya kwararru da suka taimaka wajen haihuwa,yawan yara jarirai dake mutuwa bayan haihuwa,kwayoyin da ake amfani dasu wajen hana haihuwa,tsarin kayyade iyali da kuma adadin wadanda ke haihuwa daga cikin balagaggu.
Kasashe masu tasowa da basu cimma wani nasara ba sun hadar da Bostwana,Namibia,Senegal,da Afrika ta kudu .Tun a shekarata 1994 ne kasashen Burkina faso da Camerou sukayi watsi da wannan batu.Inda aka samu cigaba tun daga wannan lokaci kuwa sun hadar da Tunisia,Bangaladash,Nepal,Peru,da Philipines.Bugu da kari rahotan yayi nuni dacewa har kasashen da suka cigaba kamar Amurka da Portugal da Kuwaiti,basu samu wani cigaba ta wannan bangare.
Wani abu muhimmi da rahotan yayi nazari akai shine yawan yammata kana dake haihuwaa janhuriyar democradiyyar congo,da Angola da Niger da Somalia da Saleon,inda kashi daya daga cikin 5 na yammata masu shekaru tsakanin 15 zuwa 19,ke haihuwa akowace shekara.A kowace shekara inji rahotan akalla mata dubu 525 ke haihuwa daga matsaloli daban daban dake tattare da ciki ko kuma lokacin haihuwa,akasarinsu kuwa daga kasashe masu tasowa.
A shekaru 10 da suka gabata ,anyi kokarin aiwatar da dokar haramta zub da ciki,amma duk da haka kowane daya daga ciki masu juna biyu 10 ,suna karewa da lalacewar cikin,a kowace shekara kuwa kimanin million 19.Kiyasin na nuni dacewa akowane minti 7 ,mace mai juna biyu guda na rasa ranta,kusan dubu 70 kenan a shekara,daga zub da ciki.A nahiyar Afrika kowace daya daga cikin mata 150 dake zub da ciki ko ke lalacewa na rasa ranta,idan aka kwatanta da guda daga cikin dubu 85 akasashen da suka cigaba.
Akasarin asibitocin kasahen duniya basu da kwararrun kayayyakin aiki na kula da lafiyan mata masu juna biyu,wadanda keda muhimmanci wajen kare su matan,wanda bazai kasa nasaba da rashin kudi,da halin ko oho da hukumomin kasashen ke nunawa kann wanan bangare ba.
Ya zuwa yanzu dai an hakikance cewa yawan yara maza dake samun shiga manyan makarantu ya dara na mata nesa ba kusa ba,amma ayanzu dai yammatan sun yunkuro a sassa daban daban na duniya.Ilimin ya mace yana da muhimmanci,domin yana rage adadin yawan yara mata dake daukan ciki da haihuwa a kowace shekara.
Zainab Mohammed.