Taron neman hada kan jam'iyyar APC
March 24, 2016Kasa da shekara guda da hawansa karagar mulkin Tarayyar Najeriya, daga dukkan alamu siyasar shekarar 2019 tana shirin farawa tare da majalisar koli ta jamiíyyar APC mai mulki tace ba wata dama ta takara a zaben shekara ta 2019. Cikin tafi da tsalle murna ne dai mahalarta wani taron koli na jamíyyar APC mai mulki yace yaji ya gani, ya kuma amince ga shugaban kasar ya zarce kan mulki a wani taronsu a nan Abuja. Duk da cewar dai basu taru da nufin yanke hukunci na siyasa ba, shugabannin jam‘iyyar a fadar sakatarenta na kasa Maimala Buni Yadi, sun gamsu da yanda yake tafiyar da kasar a halin yanzu, abun kuma da ya sa su yanke hukuncin tafi da shewa ga shugaban kasar.
To sai dai kuma koma menene tasirin matsayin da daga dukkan alamu ke zaman aiken sako ga masu sunsuna, al‘amura dai a cikin APC na dada kara baki, kama daga rikicin cikin gida zuwa asarar zabe a matakai daban daban. Tun bayan nasarar Kogi dake zaman irin ta ta farko ga limaman sauyin tun bayan zabe na kasa, ya zuwa yanzu dai jam‘iyyar ta fadi kaso 90 cikin 100 na zabukan maye gurbin da aka kai ga gudanarwa cikin kasar. Ra‘ayi kuma na rabe tsakanin masu kallon sakamakon a matsayin alamun dawowa daga rakiyar tsintsiyar da kuma masu fassarar tsohuwar al‘adar da cewar Senata Ali Ndume dake zaman dan kwamitin kolin APC ya sa su asara babba.
Duk da cewar APC na lashe rauni dama nazari na asara babba a fadar babban jagoranta kuma shugaban kasar abun da ya faru bayan zabukan na zaman abun kunyar da gwamnatinsa ba zata lamunta ba.
„Ina roko ga shugabannin sojoji da na jami‘an tsaro, dama hukumar zabe da su sani cewar ina son yan Najeriya su tuna dani ko da zan bar kujerar shugaban kasa a gobe, cewar ina mutunta su. Ina son yan Najeriya su dauki katunan zabensu a matsayin nasu kuma suna da yancin yanda suke so dashi. Imma sun ga dama suna iya sayar dashi ga wanda suke so domin dai yancinsu ne. Su sayar in yaso su zauna a gida. Amma dai ina son jami‘n tsaro su basu kwarin gwiwar cewar ba wanda zai fito don yana da kudi ya dauki ‚yan daba ya basu makamai domin su tsorata su, tare da hana su babban yancinsu ``
Abun jira a gani dai na zaman irin matakan da gwamnatin APC ke shirin dauka da nufin kawo sauyi a cikin tsarin zaben kasar da har yanzu ke tangal tangal.