260109 Weltsozialforum Brasilien
January 27, 2009Ƙungiyoyin da ke shirya wannan taro dai sun yi imani cewa, ba wai manya-manyan harkokin kasuwanci ne kaɗai za su kawo canji mai kyau ga wannan duniya ba. A kan haka ne ma suke sukar tsarin nan na mai da duniya bai ɗaya, tare da yin kira da babbar murya ga ƙasashe masu arzikin masana'antu da cewa, su sake salo, su dawo su tsara tattalin arzikin duniya yadda jama'a da kuma gwamnatocin ƙasashe matalauta za su inganta.
Alexis Passadakisa jami´ ne na wata ƙungiya daga Jamus ya bayyana dalilinsu na zaɓar birnin Belem na ƙasar Brazil domin yin wannan taro na su.
Ya ce: "Na farko dai mun zaɓi yin wannan taro a nan ne saboda yankin ƙasashen Latin Amirka sun fi ko'ina fama da bala'in yanayi duniya. Amma kuma ba a cika ba su wata kyakkyawar kulawa ba. Dalili na biyu kuma shi ne cewar, a wannan yanki akwai ingantaccen tsarin siyasa da zamantakewa, kuma ita ce da ma manufar taron da muke yi na duniya akan kyautata rayuwar al'umma".
Burin wannan taro dai shi ne a canja manufar mai da duniya bai ɗaya daga tafarkin da ake tafiya yanzu zuwa tsarin da zai kasance mafi adalci, wanda zai samar da kyakkyawa kuma ingantaccen tsarin kasuwanci na duniya, da zai ba da dama ga matalautan ƙasashe suma su bunƙasa kansu.
Fransisco Chiko Whitaker na daya daga cikin mayan da suka shirya taron;
Ya ce: "Yanzu akwai sabbin hanyoyi: Misali Yawancin al'ummar ƙasashen Latin Amirka mutane ne masu jajirce domin neman na kansu, to amma duk a banza, matuƙar dai akwai wani tsari da yake yin tarnaƙi ga hakan. Mun san cewa abin ba zai canju rana ɗaya ba, to sai dai muna bukatar wani tsari da zai baiwa mutane rayuwarsu a hannunsu, amma ba kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi ba".
Whitaker ya ci-gaba da cewa:
"Fiye da batutuwa 2000 da wannan taro na shekara ta 2009 zai tattauna akai, za su mai da hankali ne akan rikicin da ke tattare da wayewar duniya. Domin yanzu a dabaibaye muke da rikice-rikice. Kuma ya zama wajibi a lalubo bakin zaren warware su".
Kasancewar wannan shi ne karo na 9 da ake gudanar da wannan taro, Whitaker ya bayyana shirinsu na yin waiwaye adon tafiya.
Ya ce: "A wannan karon za mu waiwayi tarurrukan da muka yi tun kafuwar wannan tafiya shekaru 9 da suka wuce, domin mu duba nasarorin da muka cimma da kuma ƙalubalen da ke gabanmu. Burinmu dai shi ne kowanne ɗan Adam a wannan duniya tamu ya samu gudanar da rayuwarsa cikin walwala da ´yanci".
A duk shekara dai, masu shirya wannan taro, sukan zaɓi ranakun taron ne, dai dai da na taron shugabannin duniya akan tattalin arziki, domin su dusashe taron shugabannin duniyar, su kuma raba hankalin kafafen yaɗa labarai.