Taron kasashen Larabawa a kan makomar Siriya
December 14, 2024Taron da zai gudana ba tare da samun halartar wani dan Siriya ba, ministan harkokin kasashen ketare na Jordan da ke karban bakuncin taron, ya ce sun kira shi ne domin lalubo hanyoyin da za a taimaka wa Siriya da al'ummarta kafin a kai ga samar da wata sabuwar gwamnati.
Taron zai sami halartar ministoci daga kasashen Saudi Arabia da Iraki da Lebanon da Masar da Haddadiyar Daular Larabawa da Baharain da Qatar.
Shugabanin na kasashen Larabawa za su gana da takwarorinsu na Turkiyya da Amurka da ma wakili daga kungiyar Tarayyar Turai hadi da jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Siriya.
A makon da ya gabata ne gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen Siriya suka hambarar da tsohon Shugaban kasar Basahr al-Assad wanda ya kawo karshen shekaru 54 na mulkin sa da na mahaifinsa.
Karin Bayani: Ina makomar Siriya bayan kifar da gwamnati?