1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Hukumar IAEA kan Iran a birnin Vienna.

February 3, 2006

A yau ne za a kammala taron da Hukumar IAEA ta fara don tattauna batun makamashin nukilyan Iran da ake ta korafi a kansa. Bisa dukkan alamu dai, za a sami rinjayin masu goyon bayan zartad da kudurin kai karar Iran gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Idan ko hakan ya wakana, Iran ta yi barazanar yin watsi da kiyaye duk ka'idojin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukilyan ma gaba daya, abin da zai janyo korar duk sifetocin bincike na Hukumar IAEA din ke nan daga kasar.

https://p.dw.com/p/Bu1q
Mohammed El-baradei, shugaban Hukumar IAEA.
Mohammed El-baradei, shugaban Hukumar IAEA.Hoto: AP

Jami’an diplomasiyya a birnin Vienna, na nan na ta muhawara kan kudurin da taron Hukumar Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ke niyyar zartawa game da batun Iran. Bayan muhawarar ne za a ka da kuri’a domin zartad da kudurin. Tuni dai, kasashen kungiyar Hadin Turai, a cikinsu kuwa har da Jamus a sahun gaba, sun nanata cewa ba za su nuna sassauci a kan muhimmiyar bukatarsu ba, wato ta neman Iran ta soke duk wasu shirye-shiryen ayyukan da take yi na inganta sinadarin yureniyum. Bugu da kari kuma, sun yi kira ga shugaban hukumar IAEA din, Muhammad El-Baradei, da ya mika duk wasu rahotanni da kudurorin da aka zartar kan Iran din ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. To sai dai, Rasha ta ce ba za ta goyi bayan daukan wasu matakan takunkumi kan gwamnatin birnin Teheran ba. A ganinta dai, ya kamata a ci gaba da tattauna wannan batun a Hukumar ta IAEA. Ba ta ga dalilin janyo kwamitin sulhu a cikin maganar ba, balantana ma a yi zancen sanya wa Iran din takunkumi.

Ko wane irin kuduri aka zartar a taron na Vienna dai, babu wani abin da zai wakana kafin ran 6 ga watan Maris. A wannan ranar ne shugaban Hukumar IAEA din, Muhammad El-Baradei, zai gabatad da cikakken rahotonsa a kan wannan batun. A yanzu din ma dai, da akwai wasu batutuwan da ba a samu haske a kansu ba tukuna, inji El-Baradei; kamar wasu rahotannin da aka gabatar masa a kan wasu kafofin binciken nukilyan Iran din, wadanda ake zaton za a iya yin amfani da su wajen kera bamabamai. Kafin dai, a sami cikakkun bayanai kan wadannan kafofin, ya yi kira ga Iran din da ta dakatad da duk wasu ayyukan inganta sinadarin yureniyum din. Jakadan Rasha a cibiyar Hukumar ta IAEA, Grigorij Berdjennikov ya bayyana cewa, har ila yau dai da alamun Iran za ta amince da shawarar da kasarsa ta gabatar a taron, ta bai wa masana kimiyyan Iran din damar gudanad da ayyukan sarrafa sinadarin yureniyum a Rashan, tare da hadin gwiwar takwarorinsu na kasar. Kamar yadda ya bayyanar:-

„Har ila yau dai muna ci gaba da tuntubar Iran a kan wannan batun. Kuma matsayinta game da shawarar da muka gabatar, wani abu ne mai karfafa zuciya. A karo na farko dai mahukuntan kasar sun nuna amincewarsu da shawarar, kuma sun ce a shirye suke su shiga tattaunawa mai zurfi, don tsara yadda za a tafiyad da wannan aikin. Wannan kuwa, ai matsayi ne kyakyawa. Saboda kafin dai a cim ma ko wace yarjejeniya ma, kamata ya yi, a tattauna duk gundarin lamarin dalla-dalla. Hakan kuma na daukan lokaci mai tsawo.“

Ita ma Rashan dai na kira ga Iran da ta dakatad da ayyukan inganta sinadarin yureniyum din a mataki na farko.

A halin da ake ciki a Viennan dai, jakadan Iran a Hukumar ta IAEA, ya gargadi wakilan kasashen da ke son kai batun gaban kwamitin sulhu da cewa, za su yi wani babban kuskure na tarihi, idan suka zartad da kudurin daukan wannan matakin. Teheran dai ta yi barazanar yin watsi da ka’idojin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukilyan, abin da kuma zai kunshi korar sifetocin Hukmar IAEA din daga kasar.

Game da wannan barazanar dai, shugaban Hukumar, El-Baradei ya bayyana cewa:-

„Ina fata dai, ko wane sakamako aka ta shi da shi a wannan taron, Iran za ta ci gaba da ba mu hadin kai, don mu iya haskaka wasu tambayoyi da har ila yau ke cikin duhu. Akwai kuma wasu batutuwan da suka shafi yin amfani da makashin nukilyan ta hannunka mai sanda. To duk wani hadin kan da Iran za ta ba mu wajen warware wannan matsalar, zai janyo fa’ida gare ta da kuma gamayyar kasa da kasa.“