Taron hukumar IAEA dangane da rikicin nukiliyar Iran
February 3, 2006Kafofin yada labaru sun rawaito cewar bisa ga dukkan alamu hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA zata yi karar Iran a gaban kwamitin sulhu na MDD a dangane da shirinta na nukiliya da ake takaddama akai. A wani lokaci yau juma´a ake sa rai hukumar zata yanke shawarar akan wannan bau. A jiya alhamis shugaban hukumar ta IAEA Mohammed El-Baradei ya ce yanzu takaddamar ta kai kololuwarta, to amma hakan ba ya nufin an kawo karshen kokarin warware wannan rikici ta hanyoyin diplomasiya. El-Baradei ya ce Iran na da wa´adin wata daya na canza matsayin ta kana kuma ta dakatar da duk aikace aikace na sarrafa sinadarin uranium. Wakilan hukumar ta IAEA na tattaunawa a birnin Vienna akan wani daftarin kuduri da kasashen Jamus, Faransa da Birtaniya suka gabatar, wanda ke samun goyon bayan Rasaha da China.