Taron Hukumar IAEA a birnin Vienna.
February 2, 2006Kwamitin mashawarta na Hukumar Makamshin Nukilya ta kasa da kasa, na fara taronsa yau a birnin Vienna, inda batun makamashin nukiliyan Iran ne na farko a kan ajandar tattaunawar da za a yi. Amirka da kasashen kungiyar Hadin Kan Turai dai, wadda Jamus da Faransa da Birtaniya ke jagorancinsu a kan wannan batun na zargin Iran din ne da kokarinn yin mafani da fasahar nukiliyan wajen sarrafa makaman kare dangi.
A nata bangaren kuma, Iran ta yi barazanar bunkasa shirye-shiryenta na sarrafa sinadarin yureniyum, wanda sandunansa ne tushen samad da makamashi, amma kuma wadanda za a iya yin amfani da su wajen kera atam bam.
Da aka bude taron dai, wakilin Iran ya shiga zauren ne ba tare da yin wani jawabi ga maneman labarai ba. Masharhanta sun ce yana fatar samun goyon bayan rukunin kasashen `yan ba ruwanmu. A kalla dai, haka ne wasu maneman labarai suka ari bakinsa yana mai fada alokacin da ya zo wucewa zuwa zauren taron. A halin yanzu dai, ana ganin cewa, masu adawa da Iran din ne ke da rinjayi a taron kwamitin.
Ita dai Amirka da kuma kungiyar Hadin Kan Turai, sun yunkuri samun angizo kan kasashen `yan ba ruwanmu, bayan da suka shawo kan Sin da Rasha su goyi bayan nasu ra’ayin. Rahotanni sun ce ya da safen nan, kafin a bude taron, sai da rukunin kasashen Yamman, karkashin jagorancin Amirka, suka gana da wakilan kasashen `yan ba ruwanmun. Har ila yau dai, ba a sami tabbas kan matsayin da wasu kasashe na rukunin za su dauka ba. A lal misali ko za a sami amincewar Afirka Ta Kudu ko kuma Indiya game da tsarin kudurin da wakilan EUn a cikinsu har da Jamus da kuma Amirka suka gabatar.
Wani jami’in diplomasiyyan Jamus na kyautata zaton cewa, za a sami rinjayi kan bukatun da suka gabatar. Su dai kasashen Yamman na son a tilasa wa Iran ne da ta dakatad da duk wasu ayyukan da take yi na sarrafa sinadarin na Ureniyum, sa’annan ta kuma amince da duk wani binciken da jami’an Hukumar IAEA din z ata gudanar a cibiyoyin nukilyanta. A halin yanzu dai, rukunin Yamman na kokarin ganin an zartad da kudurin ne a tarukan na yau da gobe, inda daga bisani kuma, hakan zai bai wa shugaban Hukumar IAEA din, Muhammad El-Baradei, damar kai batun gaban kwamitin sulhu na Majalisar dinikin Duniya. Har ila yau dai, ba a sank o wane lokaci ne za a zartad da kudurin ba. Kamar yadda wani kakakin Hukumar IAEA din, Marc Widricair ya bayyanar:-
„Yadda aka shirya tsarin taron dai shi ne: Da farko kwamitin mashawartan zai yi nazari ne kann kudurin. Sa’annan a yi muhawara a kansa. Bayan wani dan gajeren hutu kuma, za a sake dawowa a yi shawarwari kan duk wata kwaskwarimar da za yi wa kudurin. Daga bisani ne kuma shugana IAEA din zai yi jawabinsa.“
Jami’an bincike na IAEA din dai, sun kasance a Iran har zuwa wasu `yan kwanaki da suka wuce. Sun dai yi koke-koken cewa, ba a ba su damar tattaunawa da wani muhimmin masanin kimiyya na kasar ba. Kuma bas u sami bayanai kan asalin na’urori da yawa na cibiyar sarrafa mamamashin nukiliyan kasar ba. Sun kuma ce lalle ne Iran na gwajin sarrafa sinadarin Yureniyum. Sai dai, sun ce ba z ata iya bunkasa wannan aikin kamar yaddda ta yi barazanar yi, idan aka kai wannan batun gaban kwamitin sulhun ba.
A halin yazu dai, jamia’n diplomasiyya na kira ga Teheran ne da ta bude duk kofofin tattaunawa da mahukuntanta a kan wannan batun. Wata hanyar warware rikicin ne dai, amincewar da shawarar da Rasha ta gabatar na gudanad da aikin sarrafa yureniyum din Iran a kasarta. Bayan haka ne za a mika wa ita Iran din sandunan da ake bukata wajen samad da makamshin.
Ana dai kyautata zaton cewa, a cikin watan Maris ne kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya zai takalo wannan batun. Kafin hakan dai, ana jira a ga cikakkun bayanan da rahoton shugaban na Hukumar ta IAEA, El-Baradei, zai kunsa.