1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hadin-gwiwar Rasha da EU

June 4, 2012

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) tana ganawa da shugabannin Rasha a garin St. Petrsburg inda za su mai da hankali kan rikicin Siriya

https://p.dw.com/p/157nG
Russian President Vladimir Putin, center, European Commission President Jose Manuel Barroso, right, and European Council President Herman Van Rompuy walk during the Russia EU Summit at the Konstantin palace in St. Petersburg, Russia, Monday, June 4, 2012. (Foto:Dmitry Lovetsky/AP/dapd)
Vladimir Putin(tsakiya) da shugabannin EUHoto: dapd

Shugaban kasar Rasha, Vladimr Putin ya jagoranci bukin bude taron hadin-gwiwa tsakanin kasarsa da Kungiyar Tarayyar Turai a garin St. Petersburg. Yayin wannan taro shugaban majalisar Kungiyar Tarayyar Turai(EU), Herman Von Rompuy da shugaban hukumar zartarwar kungiyar, Jose Manuel Barosso za su tattauna tare da Putin inda ake sa ran za su shawo kansa ga bukatar ba da taimako wajen yin kira ga shugaba Bashar al Assad da ya sauka daga karagar mulki.

A cikin jawabinsa na bude taron shugaban na Rasha ya yi magana game da bukatar kau da karbar visa tsakanin kasashensu wanda in ji shi ke karan tsaye ga yin aikin hadin-gwiwa tsakaninsu. A yammacin jiya ne yayin wata liyafa aka bude wannan taro da ke samun halartan kantomar Kungiyar Tarayyar Turai kan manufofin ketare, Catherine Ashton da shugaban hukumar makmashin kungiyar, Guenther Oettinger.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammed Nasiru Awal