1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G7 da yaki da ta'addanci a Afirka

Mohammad Nasiru AwalJune 12, 2015

Taron kungiyar G7 da alkawuran taimakawa a yakin da ake yi da tarzoma a Afirka da cin hanci a FIFA sun dauki hankalin jarudun na Jamus.

https://p.dw.com/p/1Fg86
G7 Gipfel Schloss Elmau Merkel mit Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/C. Hartmann

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus ne da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta mayar da hankali kan taron kungiyar G7 da Jamus ta dauki nauyin gudanarwa. Jaridar ta fara ne da cewa taron kolin Merkel kan Afirka sannan sai ta ci gaba tana mai cewa.

Muhimman batutuwa na duniya suka mamaye zauren taron kolin na shugabannin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, amma wani batu da ya dauki hankalin shugabar gwamnatin Jamus shi ne nahiyar Afirka, musamman kan tsaro da cututtukan da ake fama da su a yanayi na zafi da Ebola sai kuma yunwa. Saboda haka idan da wata gudunmawa da kasashe masu arzikin masana'antu za su bayar don rage yawan masu fama da matsalar yunwa a duniya, Afirka za ta fi ci moriyar wannan tallafi. Rage yawan mayunwata da inganta yanayin rayuwa da na aiki musamman ga mata da kuma samun karin kudin shiga zai taimaka wa gwamnatoci tare da rage yawan masu sha'awar yin kaura zuwa Turai. Hakazalika sahihan manufofin kare muhalli za su taka muhimmiyar rawa bisa manufa domin miliyoyin mutane a Afirka sun shiga mawuyacin hali sakamakon matsaloli masu nasaba da sauyin yanayi.

Yaki da 'yan tarzoma a Afirka

Kungiyar tarayyar Afirka ta daura damarar yaki da ta'addanci inji jaridar Neues Deutschland a labarin da ta buga game da taron kolin kungiyar ta AU a ranakun 10 zuwa 12 ga watan nan na Yuni a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Symbolbild Soldaten Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Ta ce da farko an yi fargabar cewa da yawa daga cikin mahalarta taron za su kaurace masa saboda boren kyamar bakin da ya auku a Afirka ta Kudu cikin watan Afrilu, inda aka kashe 'yan Afirka da dama sannan dubun dubatan suka tsare daga kasar. Rikice-rikice da yake-yake da kuma tarzoma suka mamaye ajandar taron. Sai kuma rikicin siyasar kasar Burundi, inda shugaba Pierre Nkurunziza ke neman wa'adin mulki karo na uku, matakin da ya jefa kasar cikin rudani. Hakazalika yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram a Najeriya na daga cikin jadawalin taron. Jaridar ta ce saboda wadannan rikice-rikice ya sa ainihin babban batun da ke samar ajandar taron wato "Shekarar Mata da kuma tsarin ci-gaban Afirka zuwa shekarar 2063" ya koma sahun baya.

Blatter ya san da miliyan 10 daga Afirka ta Kudu

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tsokaci ta yi game da badakalar cin hanci da ta dabaibaye hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, inda ta yi magana game da dala miliyan 10 da Afirka ta Kudu ta ba wa FIFA.

Bildergalerie Joseph Blatter
Sepp Blatter a dama da tsohon shugaban Afirka ta Kudu marigayi Nelson MandelaHoto: picture-alliance/dpa/E. Risch

Ta ce hakika shugaban FIFA Sepp Blatter na da sanin cewa Afirka ta Kudu ta saka kudaden a asusun ajiyar tsohon jami'in FIFA kuma dan kasar Trinidad and Tobago Jack Warner. Sai dai Warner wanda a lokacin yake rike da mukamin mataimakin shugaban FIFA ya musanta zargin cin hanci da rashawa. Ita ma FIFA ta ce ko kadan dala miliyan 10 daga Afirka ta Kudun ba goro ba ne na ba ta damar daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafar duniya a shekarar 2010. Sai dai wani aikin alheri ne da nufin bunkasa wasan kwallon kafa a yankin Karibik.