1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G20 a Faransa

February 19, 2011

Ƙasashen G20 sun kasa cimma daideto kan matsalar ƙaruwar farashin kayan masarufi a taron da suke yi a Faransa.

https://p.dw.com/p/10KSF
Shugaba Nicolas Sarkozy,(farko daga dama) yana jagorantar taron G20Hoto: AP

Ƙasashen G20 masu ƙarfin tattalin arziƙi waɗanda suka fara taron tsawon kwana biyu daga ranar 18 ga watan Fabrairu a birnin Paris na ƙasar Faransa, ba su cimma matsaya ba dangane da ƙudurinsu na samun daidaito a hauhawar farashin kayayyakin masarufi da ake samu a ƙasashen duniya. Ƙasar China dai na jan ƙafa wajen amincewa da wasu daga cikin matakan da ƙungiyar ke so ta ɗauka, ko da yake ƙasashe masu tasowa basu riga sun ɗauki wani matakin bai ɗaya dangane da batun ba.

Nicolas Sarkozy Treffen der G-20-Staaten Frankreich
Shugaba Nicolas Sarkozy yayin jawabinsa na buɗe taron G20Hoto: AP

A jawabinsa na buɗe taron shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy ya ƙalubalanci ministocin da ke wakiltar ƙasashensu a taron da su mance da banbance-banbance da ke tsakaninsu, su kuma ajiye son ransu a gefe domin amfanin jama'a da ma cimma manufofin ƙungiyar ta G20.

Sarkozy ya sha alwashin gyara tsarin kuɗin duniya, da kasuwanin kayayyakin masarufi a bana a matakin ƙungiyar ta G20, kuma ana sa ran ministocin kuɗi za su gudanar da wani taro a yau asabar domin cimma matsaya, dangane da wannan batu.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Halima Balaraba Abbas