1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G20 a Faransa

February 18, 2011

Ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi wato G20 za su gudanar da taro a birnin Paris na ƙasar Faransa don tattauna matsalar ƙaruwar farashin kayan masarufi.

https://p.dw.com/p/10JNM
Shugaba Nicolas Sarkozy, mai karɓar baƙoncin taron G20Hoto: AP

A ranar 18 ga watan Fabrairu ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a duniya wato G20 za su fara wani taro a birnin Paris na ƙasar Faransa domin duba hanyoyin daƙile matsalar hauhawar farashin kayan masarufi. Ministan aikin noma na Faransa, Bruno le Maire ya bayyana ajandar ƙasarsa a tsawon shugabancin da za ta yi wa G20 yana mai kasahedi game da yiwuwar ɓarkewar rikice-rikice a faɗin duniya sakamakon ƙaruwar farashin kayan abinci. Le Maire ya faɗa wa Majalisar Ɗinkin Duniya cewa ya damu matuƙa game da yiwuwar ƙaruwar farashin kayan abinci yana mai nuni da ƙaruwar farashin masara daga Euro 115 akan kowane ton a watan Yulin bara zuwa sama da euro260 a yanzu. Sassauta matsalar ƙaruwar farashin kayan masarufi dai na zaman ɗaya daga cikin manufofin Shugaba Nicolas Sarkozy.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu