1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARO KAN INGANTA WANI IRI NA KOFI - A BONN

YAHAYA AHMEDMarch 31, 2005

Kofi dai, ya zamo kamar wani abin al'ada ne a nan Jamus. An kiyasci cewa, kusan ko wane mutumin da ke zaune a nan kasar, na shan kofuna 3 da rabi na kofin a ko wace rana.

https://p.dw.com/p/BwUn
Manomin kofi a kasar Habasha.
Manomin kofi a kasar Habasha.Hoto: AP

A cikin wannan makon ne, masana kimiyya na fannin ilimin tsirrai, suka yi wani taron kara wa juna ilimi a nan birnin Bonn, a kan hanyoyin kare wani iri na musamman na shukin kofi , wanda masana kimiyya ke kira Coffea arabica . Daga wannan irin ne dai ake samo kashi 70 cikin dari, na duk kofin da ake kasuwancinsa a duniya.

Da farko dai kwararrun masanan sun yi nazari ne kan asalin irin wannan shukin na kofi. A daura da yadda ake zato, ba daga kasashen larabawa ne shukin ke da asalinsa ba. An fara samo shi ne a cikin tsaunukan kasar Habasha, inda da can ake da kundurmin dazuzzuka da yawa. Amma a cikin shekaru 30 da suka wuce, saboda yawan sare itatuwan da aka yi ta yi, Habashan ta yi asarar kashi 60 cikin dari na albarkar dazuzzukan da Allah ya ba ta. A halin yanzu ma dai, masana kimiyya sun kiyasci cewa, kusan kashi 4 cikin dari da na fadin kasar ne kawai, ke da daji. Hakan kuwa ya shafi wannan shukin na kofi ainun, abin da ya kai ga masana kimiyyan yin fargabar cewa, idan ba a dau sahihan matakai ba, nan gaba, irin na Coffea arabica zai kare ma daga doron kasa.

Wasu daga cikin kwararrun masanan, sun ba da rahoton ayyukan binciken da suka gudanar ne a Habashan, wato inda suka kira tushen kofin, a cikin tsaunuka da kundurmin dajin jihar nan ta Kaffa, da ke kudu maso yammacin kasar. A nan ne dai suka gano shuke-shuken kofin asali da ke tsirowa da kansu, kamar yadda halitta ta tanadar. Gaba daya dai, masana kimiyya sun ce, sun iya gano iri daban-daban dubu 4, na kofi a duniya. Amma idan aka bi diddigin duk shuke-shuken kofin da ake da su a doron kasa, wanda yawansu ya kai kusan biliyan 10, za a ga cewa, suna da asali ne daga Habashan. An dai fara gano shukin kofin ne tun cikin karni na 11 a kasar ta Habasha.

Binciken kimiyya na nuna cewa, kwayoyin hali, wato genes a turance, na kofi ba su da yawa. Sabili da haka ne, idan shukin ya kamu da wasu kwayoyin cututtuka, sai ka ga an yi dimbin asarar girbi. Masana kimiyyan, sun ce sun gano irin wadannan kwayoyin cututtukan a Habasha. Amma abin mamaki shi ne, ba sa lahanta irin kofin da ke tsirowa da kansu a kundurmin dajin kasar, a daura da sauran kofin da ake nomansu a gonaki.

Da yake gabatar da sakamakon binciken da masana kimiyyan suka gudanar, Manfred Denich, na cibiyar binciken halayyar tsirrai da ke nan birnin Bonn, ya bayyana cewa:-

"Mun san cewa, kwayoyin cututtukar kofi, ba su da wani angizo kan shukin da ke cikin kundurmin dajin Habasha. Akwai su, kuma mun gano su da yawa. Amma ba sa iya harbin wannan iri na kofi. Duk da yaduwarsu, suna nuna halin zaman cude ni in cude ka ne da shukin kofin ba tare da lahanta su ba."

Abin da masana kimiyyan suka gano kuma shi ne: Wannan iri na kofin da ake samu a kundurmin dajin Habasha, yana kuma iya jure wa fari. `Ya`yansa kuma ba su da yawan sinadarin nan na coffein. Amma kawo yanzu dai, wana dan nau’i kadan na shuke-shuken kofin ne masana kimiyya suka iya gudanad da bincike a kansa. Dalilin haka kuwa, shi ne ba a iya adana irin kofi a kankara har zuwa wani lokaci mai tsawo, kamar yadda ake iya adana irin wasu tsirrai da dama. Game da hakan dai, Manfred Denich ya kara bayyana cewa:-

"Matsalar da muke huskanta game da adana iri na kofin ita ce, bayan kusan watanni uku a cikin kankara a firjin, ba za su tsiro ba kuma in an shuka su. Sabili da haka ne, duk cibiyoyin gudanad da bincike kan wannan shukin, suke samo irinsu daga gonaki kai tsaye."

Game da amfaninsa kuwa, irin wannan kofin da ake samowa daga kundurmin dajin Habasha kawai, wato wani tushe ne na samun kudaden shiga, ga mazauna wannan yankin na kasar. Ba sa dai nomansa. Tsirowa yake yi da kansa a daji, sa’annan su kuma su je su tsinko, ko su yi girbinsa.

A wannan yankin dai, irin wannan kofin na da muhimmanci kwarai ga halin rayuwar jama’a. Yana kara wa kundurmin dajin daraja. Sai dai, a bangare daya kuma, yana janyo asarar dazuzzuka a ko wace shekara. Don magance wannan matsalar ne dai, masana kimiyyan cibiyar binciken halayyar tsirrai da ke nan Bonn, suka gabatad da wani shiri na fadakad da jama’an wannan yankin na Habasha, kan muhimmancin kawo karshen sare dazuzzuka. Till Stellmacher, na cikin wadanda suka gabatar wa mazauna yankin wannan shirin. Ya bayyana cewa:-

"A dajin da ake tsinko irin wannan kofin, mun bayyana musu cewa, kada su sare ko wane itacen da shukin kofin ke karkashinsa, saboda idan sun yi hakan, girbin da suke samu a shekara zai ragu. Manoman da kansu ma dai suna sane da hakan. Idan ko shukin ya zamo musu wani muhimmin tushe na inganta tattalin arzikinsu, to sai ka ga cewa, sun fi kula da kare dazuzzukan."

Masana kimiyyan dai, sun samo wa manoman wannan yankin kasuwar irin nasu kofin a nan Jamus. A shekarar bara kawai, kusan tan 90 na irin wannan kofin ne aka shigo da shi nan kasar. Saboda bambancinsa da sauran ire-iren kofin da ake shukawa, ya sa kudinsa ma ya tashi a kasuwannin duniya. A nan Jamus dai, kudin ko wani paki na wannan kofin, mai nauyin giram dari 2 da 50, ya kai Euro 6 da santi 25. Abin da ke da muhimmanci kuwa a nan shi ne, kago wata hanya ta bambanta wannan irin da sauran da ake samu a ko’ina. Masana kimiyyan dai sun ce sun cim ma nasarar kago wannan fasalin. Kamar yadda Rolf Willmund ya bayyanar:-

"Mun kago wata fasaha, ta iya gano kofin da ke da asali daga wannan yankin na Habasha. Fasahar na iya ba mu damar bambanta wannan irin da sauran duk kofin da ake da shi a duniya. Kai a Habashan ma, duk wani irin daban da aka samo daga wani yanki mai nisan kimanin kilomita dari daga harabar da muke aiki, za mu iya bambanta shi, ta hanayar wannan fasahar. Balanta kuma a ce, wani irn kofin ne daga Brazil ko wasu yankuna daban na Afirka. Wannan aiki ne mai sauki gare mu."

An dai kiyasci cewa, ko wane bajamushe na shan kofuna 3 da rabi na kofi a ko wace rana a nan kasar. Hakan kuwa, idan aka dau jumlar kofin da ake sha a ko wace rana a nan Jamus, ya kasance rabi ke nan na duk kofin da ake samowa a duniya baki daya.