Taro game da matsalar kyamar baki a Jamus
November 18, 2011Talla
Ministocin shari'a da na cikin gida, na jihohin Jamus gaba daya, tare da gwamnatin Tarayya sun fara wani zaman taro na musamman a birnin Berlin, domin tattana matsalar kyamar baki da wasu jamusawa masu akidar Hitler ke nunawa baki 'yan kaka gida dake Jamus.
A baya bayan nan, wannan matsala ta mamaye fagen siyasar Jamus bayan da aka gano wani gungun tsirarun mutane masu tsatsauran akidar Nazi da suka hallaka baki Tara daga shekara 2000 zuwa 2007.
Albarkacin wannan taro, ministocin za su tattana hanyoyin karfara doka da kuma matakan tsaro.A wani bayani da ta gabatar, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ,ta dangata kyamar baki a matsayin abun kunya ga kasar Jamus.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman