Tarihin wasannin kwallon kafa na Bundesliga a Jamus
Hotunan da suka fi daukar hankali, da ba da mamaki da ban dariya da sanya tunani mai zurfi a tsawon shekaru 50 na lig-lig, wato Bundesliga.
Cin kwallo na farko a Bundesliga
Lokacin da aka kirkiro wasannin Lig na Bundesliga a bazarar shekara ta 1963, 'yan dakikoki kawai aka dauka, kafin Friedhelm "Timo" Konietzka ya ci kwallo ta farko. Saboda masu daukar hoto ba su shirya ba, babu hotunan wannan ci, inda Konietzka ya jefa kwallon lokacin karawa tsakanin kungiyarsa ta Borussia Dortmund da Werder Bremen. Wadannan kungiyoyi biyu har yanzu suna nan a Bundesliga.
Kungiyar da ta fi rashin nasara
A shekara ta 1965 lokacin da aka kori kungiyar Hertha BSC daga Bundesliga saboda biyan 'yan wasa kudin da ya wuce kima, hukumar DFB ta nuna bukatar samun wata kungiyar daga Berlin a Bundesliga, ta tilasta wa Tasmania 1900 zuwa rukuni na daya amma ta kasa gogayya da sauran kungiyoyi. Ya zuwa yau, Tasmania ita ce ta fi rashin nasara a tarihin Bundesliga inda ta zama ta karshe a kakar.
Cizo a inda bai dace ba
Wasan makwabta tsakanin Dortmund da Schalke a watan Satumba shekara ta 1969, ya zama abu na musmman. Bayan da aka ci daya da nema, 'yan kallo sun kutsa filin wasa har suka tsorata karnukan masu gadi, wadanda suka kai wa 'yan wasan Schalke Friedel Rausch da Gerd Neuser cizo a mazaunai da katarensu. Bayan allurar Tetanus, Rausch ya ci gaba da wasa amma tabon cizon har yanzu yana nan.
Rushewar gidan mai tsaron gida
A watan Aprilu shekara ta 1971, dan guntun katako ya shiga tarihi: Lokacin karawa tare da Bremen, dan wasan Mönchengladbach Herbert Laumenya fada ragar mai tsaron gida, abin da ya kawo rushewar katakon gidan gaba daya. Duk da kokarin da aka yi na gyara abin bai yiwu ba, inda aka dakatar da wasan da ci daya da daya, amma daga baya aka ce Bremen ta sami nasara da ci biyu da nema.
Abin kunya a Bundesliga
A bikin cika shekarunsa 50, shugaban kungiyar Kickers daga Offenbach, Horst Canellas ya yi wa bakinsa ba-zata da maganganun wayar tarho dake nuna hada bakin magudi da cuta a wasannin wasu kungiyoyi na neman kauce wa zuwa rukuni na biyu a kakar 1970 zuwa 1971. Abin kunyar ya sanya aka dakatar da 'yan wasa da masu koyarwa da shugabanni. Kungiyoyin Offenbach da Bielefeld aka saukesu daga Bundesliga.
Kundin Tarihi
Kungiyar Eintracht Braunschweig ita ce ta farko da ta sanya talla a rigunan 'yan wasa, wato hoton kan barewa na kamfanin "Jägermeister". Tun kafin hakan sai da aka yi watanni ana takaddama, saboda hukumar DFB ta ki yarda a maida 'yan wasa su zama kamar wasu allunan talla. A karshe tilas DFB ta mika wuya. Bayan shekaru takwas, babu wata kungiya a nan Jamus da ba ta da talla a rigunan 'yan wasa.
Alkalin wasa mai kiyaye lokaci
A watan Nuwamba shekarar 1975, alkalin wasa Wolf-Dieter Ahlenfelder ya tura 'yan wasa zuwa hutun rabin lokaci bayan minti 32 kawai. Dalilin hakan shi ne: tun kafin wasa sai da ya ziyarci gidan shan barasa, ya cika cikinsa kafin ya shiga fili. Ya ce, "Mu maza ne kuma maza ba sa shan Fanta!" Ko a yau, mutum yana iya sayen samfurin barasa mai suna "Ahlenfelder" a wasu gidajen shan barasa na Bremen.
Nasarar cin kwallo mafi girma
A karshen kakar 1978, kungiyar FC Cologne da mai bin bayanta Mönchengladbach sun yi gwagwarmaya da juna. Kafin wasan karshe kungiyoyin suna da maki daidai, to amma Cologne tana da cin kwallo 10 fiye da Gladbach, da ta yi iyakacin kokarin zama zakara a karshen kakar, inda ta lashe Dortmund da ci 12 da nema. Duk da haka Cologne ta sami nasarar wasanta da ci biyar da nema ta kuma zama zakara.
Tabo mafi tsawo
A watan Agusta shekara ta 1981, dan wasan Bremen Nobert Siegmann ya ji wa Ewald Lienen na Bremen rauni tare da tabo mai tsawon cm 25 a katarensa. Lienen ya fuskanci mai koyar da Bremen, Otto Rehhagel inda ya zarge shi da laifin jan hankalin dan wasansa yayi masa keta. Lienen ya koma wasa daga baya amma Rehhagel ya fara samun barazana har ma a wasa a Bielefeld sai da ya sanya riga mai sulke.
Fanarite mafi suna
A wasannin mako na 33 a kakar 1985 zuwa 1986, inda Michael Kutzop ya ci bugun daga kai sai mai tsaron gida saura minti daya a tashi a karawa da Bayern Munich da Bremen ta zama zakara a kakar amma Kutzop ya sanya kwallon ta bugi katakon mai tsaron gida, aka tashi babu inda aka ci. A ranar karshe Bremen ba ta sami nasarar wasanta ba inda Munich ta yi farin cikin zama zakara.
Cin kwallon da ba ci ba ne
A watan Aprilun 1994 lokacin wasa tsakanin Nuremberg da Bayern Munich, dan wasa Thomas Helmer ya buga kwallon da ta wuce ta gefen gidan gola. Alkalin wasa ya ce an ci, inda tun daga nan aka kirkiro kalmar "Phantomtor", wato cin kwallon da ba ta shiga ba. Nuremberg an lashe ta da ci biyu da daya, kuma sami daukaka kara daga baya. A wasan da aka maimaita Nuremberg ta sha kaye da ci biyar da nema.
Fushin mai koyarwa
A watan Maris shekarar 1998, mai koyar da Bayern Munich, Trappatoni ya nuna fushinsa a bainar jama'a. Ya sha kare 'yan wasansa saboda kokarinsu a filin wasa. A sanannen jawabin nan da yayi cikin fushi, Trappatoni, ya yi amfani da kalmomi kamar: "Mai koyarwa ba wawa ba ne!" "Wadannan 'yan wasa sun yi wasa kamar kwalbar da babu komai cikinta!" ko "Na kare!" A karshe dai kowa ya gane manufarsa.
Kungiyar baki zalla
A watan Aprilun shekara ta 2001, kungiyar Energie Cottbus ta tura 'yan wasa 11 da babu Bajamushe ko daya cikinsu a filin wasa. Wasan tsakaninta da Wolfsburg an kare shi ne babu inda aka ci, amma ya shiga kundin tarihi. Sunayen 'yan wasan na Cottbus: Piplica, Hujdurovic, Matyus, Akrapovic, Kobylanski, Latoudji, Miriuta, Reghecampf, Vata, Franklin da Labak
Zarakun Bundesliga a badini ba na zahiri ba
Tare da imanin cewar sun zama zakarun Bundesliga karon farko bayan shekara ta 1958 'yan wasan Schalke sun fara murnar nasararsu tare da 'yan kallo a filin wasa, ba su san cewar ba'a kare wasa tsakanin Bayern Munich da Hamburg ba. Dukkan 'yan kallon Shalke suna gani a katon allon bidiyo Bayern Munich ta rama cin da aka yi mata, kuma ta zama zakara. Bayern tana farin ciki, Schalke tana kuka.
Fuskar kwallon kafa mai muni
Tun daga 'yan watannin baya ake ta samun al'amura marasa kyawun gani a filayen wasannin kwallon kafa. 'Yan kallo sukan kunna haramtattun kayan wasan wuta, ko kuma samun tashe-tashen hankula masu tsanani. Hukumar DFB ta kan yi hukunce-hukunce masu rangwame ga masu laifi. To amma hakan zai sanya a shawo kan wannan matsala?