Tarihin Kofi Annan
October 13, 2008Masu sauraronmu asalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da ke amsa tambayoyin masu sauraro.
Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito ne daga hanun mai sauraron mu a yau da kulum Saidu Gangara fada Radiyo makaranta BP 144 Maradi a jamhuriyar Niger. Mai sauraron namu cewa ya yi; bayan gaisuwa da fatan alheri, don Allah ku ba ni tarihin tsohon sakatare janar na Majalisar Dikin Duniya Kofi Anan.
Amsa: An haifi Kofi Anann ne a birnin Kumasi na ƙasar Ghana a ranar 8 ga watan Afrilun shekara ta 1938, ya kuma yi karatunsa na jami'a, a jami'ar kimiya da fasaha ta Kumasi, kuma ya kammala bincike na digirinsa a fanin ilimin tattalin arzikin ƙasa a jami'ar kwalejen Macalester dake birnin St.Paul Miniestota a ƙasar Amirka a shekata ta 1961.
Daga 1961 zuwa 1962, Kofi Anan ya yi karatu a fannin ilimin tattalin arzikin ƙasa a sashen nazarin ilimin tattalin arziki na jami'ar des Hautes Etudes Internatinale ta Geneva. A shekara ta 1971 zuwa 1972 Kofi Anan ya zamanto mutumin da ya yi karatu a kwalejen kimiya da fasaha ta Massachusetts a Amurka, anan ɗin kuma ya sami baban digiri a fannin kimiyar tafiyar da ragamar mulki.
Mr. Anan ya fara aiki da Majalisar Dinkin Duniya ne a matsayin jami‘i mai lura da harkokin gudanarwa da kasafin kuɗi, a ɓangaren hukumar lafiya ta Majalisar Dikin Duniya dake da mazaunin ta a birnin Geneva.Tun daga wannan lokacin dai Kofi Anan ya yi aiki a ƙarƙashin hukumar dake lura da bunƙasa tsarin tattalin arzikin ƙasashen Afirka dake da mazauni a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha.
Kofi Anan ya riƙi muƙamin muƙaddashin sakatare janar na hukumar tsaro da kare haƙin bil Adama ta Majalisar Dikin Duniya a tsakanin 1987 zuwa 1990.
Mr. Kofi Anan dai ya riƙi muƙamai da dama a Majalisar Dikin Duniya, kuma shi ne ke zaman mutum na bakwai a jerin mutanen da aka zaɓa kan muƙamin baban sakatare janar na Majalisar Dikin Duniya.Ya dai fara riƙe muƙamin babban sakatare janar na Majalisar Dikin Duniya karo na farko a ranar ɗaya ga watan Janairun 1997, bisa amincewar kwamitin sulhu da kuma baban zauren mashawartar majalisar. An kuma sake zaɓar Kofi Anan karo na biyu kan mukamin na sakatare janar na Majalisar Dikin Duniya a ranar ɗaya ga watan Janairun shekara ta 2002, inda ya ƙare wa'adin aikinsa a ranar 31 ga watan Decemban shekara ta 2006.
Kafin dai a naɗa Kofi Anan kan muƙamin baban sakatare janar na Majalisar Ɗikin Duniya, Anan sai da Anan ya riƙi muƙamin muƙaddashin sakatare janar ɗin Majalisar Dinkin Duniya mai lura da harkokin ayyuka na kiyaye zaman lafiya a ƙasahen duniya. A lokacin da aka cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Bosniya Hergovina, Mr Anan ya riƙi muƙamin wakilin musanman na baban sakatare janar zuwa tsohuwar Yugoslavia, inda aka ɗora masa alhakin harkokin miƙa mulki ga farar hula a Bosnia Herzgovina, domin a wanan lokacin sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dikin Duniya, ƙarƙashin shugabancin ƙungiyar tsaron tekun AtlantiKa ta Nato, aka ɗorawa alhakin gudanar da ayyuka na kiyaye zaman lafiya a Bosniya.
Mr. Kofi Anan ya yi amfani da muƙaminsa na ƙaramin sakatare janar mai lura da ayyuka na kiyaye zaman lafiya a ƙasahen duniya, wajen tabatar da zaman lafiya lokacin da aka fuskanci matsalolin tashe-tashen hankula ko siyasa a ƙasashe da dama na duniya, kamar dai shirin miƙa mulki ga hanun farar hula a Najeriya, rikicin bom ɗin yankin Lokerbiya tsakanin Amurka da Libya, sai kuma yunƙurin tabatar da zaman lafiya a gabashin Temo, tare kuma ƙoƙarin ganin an sami sulhu tsakanin Isra'ila da Palasdinawa ƙarƙashin ƙudirorin kwamitin sulhu na Majalisar Ɗikin Duniya. A watan Afrilun shekara ta 2000, Kofi Anan ya gabatar da wani rahoto, inda ya buƙaci ƙasahen duniya da su taimaka wajen gabatar da wani tsari da zai taimaka wajen yaƙi da talauci, tare da inganta manufofi na wayar da kan jama'a game da yaƙi da cutar AIDS dake damun matalautan ƙasahe masu tasowa na duniya. Mr. Anan bai tsaya a nan ba, sai da ya buƙaci ƙasashe masu arzikin masana'antu da su taimaka wajen kawo ƙarashen matsaloli na yaƙe-yaƙe da tashe-tashen hankula da ake fama da su a ƙasashe da dama na duniya.
A ranar 10 ga watan Disamban shekara ta 2001, aka baiwa Kofi Anan lambar gimamawar zaman lafiya ta ƙasahen duniya, bisa irin rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a ƙasashe da dama na duniya. Kuma a wannan shekara ta 2008 ne aka naɗa Kofi Annan a matsayin shugaban jami'ar Ghana.
Babban sakataren dai na Majalisar Dikin Duniya mutum ne da ya ƙware wajen yin magana da harshen Turanci, Faransanci da kuma wasu harsuna na Afirka. Ya auren wata mashahuriyar lauya 'yar ƙasar Sweden, kuma ta rubata littattafai da dama game da ƙananan yara da kuma Majalisar ta Dinkin Duniya. Yanzu haka dai Mr. da kuma Mrs. Anan nada yaya uku.