1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai za ta bada tallafin Euro miliyan 81 ga Afirka ta Tsakiya

March 15, 2014

Wata tawagar kungiyar Tarayyar Turai da ke ziyarar aiki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta bayyana aniyar kasashen Turan na ba da wani tallafin kudade ga wannan kasa.

https://p.dw.com/p/1BQD1
EU-Kommissar Andris Piebalgs
Hoto: picture alliance/AP Photo

Labarin ya fito ne a yammacin wannan Juma'a da ta gabata, daga membobin wannan tawaga, yayin ganawarsu da shugabar rikon kwaryar kasar Catherine Samba-Panza, a cewar wata majiya ta kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP.

Tawagar dai ta hada da kwamishinan Tarayyar Turai mai kula da bunkasar kasashe Andris Piebalgs, da ministan raya kasashe na Faransa, da kuma ministan huldodi na Jamus Gerd Müller inda suka je wannan kasa domin gane wa idanuwansu abubuwan da ke wakana.

Wadannan kudade za a yi amfani da su ne a fannonin ilimi domin farfado da makarantu, da kuma kiwon lafiya ta hanyar samar da kayayyakin aiki ga asibitoci, da fuskantar karancin abinci da ma tamowar yara kanana, tare da ganin an samu cigaban harkokin noma ta hanyar samar da irin shuki, a cewar Andris Piebalgs, kwamishinan na Tarayyar Turai mai kula da bunkasar kasashe.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal