1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Taimakon Tarayyar Turai ga 'yan gudun hijira

Suleiman Babayo LMJ
February 2, 2024

A wani mataki na maimakon Turkiyya game da 'yan gudun hijira kungiyar Tarayyar Turai ta ba da makuden kudi ga kasar Turkiyya.

https://p.dw.com/p/4bzKV
'Yan gudun hijira na kasar Siriya da ke Turkiyya
'Yan gudun hijira na kasar Siriya da ke TurkiyyaHoto: Francisco Seco/AP Photo/picture alliance

Kungiyar Tarayyar Turai ta tura kimanin Euro milyan 26 na taimakon jinkai ga kasar Turkiyya, saboda 'yan gudun hijira da ta karba galibi daga kasar Siriya bayan bayan girgizar kasa da aka samu a shekarar da ta gabata tsakanin kasashen biyu na Turkiyya da Siriya.

Karin Bayani: Miliyoyin yara na neman agaji a Siriya

A cikin wata sanarwa Janez Lenarcic kwamishinan kungiyar ta Tarayyar Turai mai kula da rikice-rikice ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Jumma'a.

Fiye da mutane dubu-50 suka halaka sakamakon girgizar kasar da aka samu a kasashen na Siriya da Turkiyya masu makwabtaka da juna. Kungiyar ta Tarayyarv Turai tana taimakawa da magunguna da kuma tsabtar muhalli.