1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Babban zaben Najeriya na 2023

Abdoulaye Mamane Amadou
June 9, 2022

A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, manya da kananan jam`iyyun siyasa a Najeriya ciki har da APC mai mulki da NNPP da PDP mai adawa, sun fitar da 'yan takara.

https://p.dw.com/p/4CUVp
Bildkombo | Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso und Atiku Abubakar

Daukacin jam'iyyun Najeriya manya da kanana sun gudanar da zabukan fidda gwani don tantance 'yan takarar da za su wakilci jam'iyyun a babban zaben Najeriya da ke tafe a shekara ta 2023. Sai dai duk da rikicin cikin gida da zargin amfani da kudi, manyan jam'iyyun siyasa irinsu APC da PDP sun tsayar da nasu 'yan takara.

Jam'iyyar APC ta zabi Sanata Bola Tinubu a matsayin dan takara, bayan da ya doke abokan karawarsa a zaben fidda gwanin da aka kammala a tsakiyar wannan mako. Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zabi Atiku Abubakar a matsayin nata dan takara don halartar zaben shugaban kasar na 2023. Jam'iyyar NNPP ta fitar da Dr Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin wanda zai tsaya mata takara a babban zaben. 

Sai dai da dama na aza ayar tambaya kan hujjojin da wakilan jam'iyyun siyasar suka yi amfani da su wajen tantance 'yan takara, ganin yadda wasu 'yan takara da dama da suka yi aiyukkan alheri a wasu yankuna ba su samu koda kuri'a daya ba.