Tallafa wa ƙasashen Afirka na UEMOA don inganta rayuwar al'umma
October 14, 2011Maƙasudin taron dai shi ne yin nazari akan jerin ƙalubalan da ƙanann hukumomin ƙasashen yankin na UEMOA su ke fuskanta a cikin tsarin kasafa yankuna ƙasa da ƙasashen nasu suke a kai tare da duba hanyoyin inganta rayuwar ƙananan hukumomin da al'ummominsu.
A ƙarkashin wani shirinta ne neman sasanta rigingimun siyasa a cikin ƙasashen duniya gidauniyar Konrad Adenauer ta tanadi wani tsari na taimakawa ƙanann hukumomin ƙasashen nahiyar afrika inda aka kaddamar da shirin kasasfa yankunan ƙasa.
Taron wanda ya hada wakillan kungiyoyin magadan gari na kasashe 8 mambobin kungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma masu amfani da kuɗi bai ɗaya na cewa wato UEMOA na da gurin garin magadan garin kasashen kungiyar da su ke halartar wannan sun tattauna domin yin masanyar bayanai ddangane da irin matsalolin da ke ci masu tuwo a kwarya cikin tafiyar da tsarin cin gashin kai ko decentralisation a faransance a cikin kasashensu da zummar samar da shawawari da za su taimaka masu wajan inganta rayuwar alummominsu.
Ko baya ga matsalar dangantaka tsakanin shugabnnin kananan hukumomi da gomnatin tarayya a cikin kasashen na UEMOA taron ya mayar da hankali kan batun wani tsari na kulla huldar dangantaka da zamantakewa a tsakanin kananan hukumomi da kungiyar ta UEMOA ke son kaddamarwa dama kuma batun girka wata babbar majalissar magadan gari na kasashen kungiyar ta UEMOA.
A ƙarshen taron dai mahalartan nasa sun sake tsayar da birnin yamai a matsayin wanda zai karbi bakuncin babban taron girka babbar majalissar magadan garin ƙasashen ƙungiyar ta UEMOA a cikin watan Nuwamba mai zuwa.
Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal