1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta kori mambobinta 3,000

Abdul-raheem Hassan
January 16, 2022

Gwamnatin Taliban na zargin wasu mambobinta da cin zarafi da ya saba tsarin shugabancin da kungiyar ta kaddamar bayan karbe mulki a watan Agusta na shekarar 2021.

https://p.dw.com/p/45b5w
Afganistan | Taliban | Kabul
Sojojin Afganistan kenan a birnin Kabul a shekarar 1996Hoto: Hurriyet/AP/picture alliance

Kungiyar Taliban ta shafe tsawon shekaru 20 tana fafutikar kwace iko da gwamnatin Afganistan, tun bayna da sojojin Amirka da NATO suka mamaye kasar don daukar fansa kan harin ta'addancin 9/11 da kungiyar al-Qa'ida ta kai Amirka.

Taliban ta ce matakin sallamar wasu jami'an nata ya biyo bayan kama su da laifin bata wa addini suna da shafawa gwamnati bakar fenti a idanun duniya ta hanyar ta'ammali da kwayoyin maye da sace dukiyar al'umma da cin hanci da rashawa da kuma hada baki da kungiyar IS.

Tun bayan da Taliban ta rusa gwamnatin dimukuradiyya a Afganistan, akwai rahotannin da ke zargin sabuwar gwamnatin da takurawa al'aumma da tauye 'yancin mata da aiki da zuwa makaranta, sai dai Taliban ta sha karyata rahotannin.