1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Afghanistan: Mata na yi wa Taliban zanga-zanga

December 28, 2021

Daya daga cikin matan da ke zanga-zanga ta ce kisan da Taliban ke yi a asirce ya saba wa alkawuransu na yi wa tsaffin jami'an gwamnatin kasar afuwa.

https://p.dw.com/p/44uwM
Afghanistan PK der Taliban
Hoto: Rahmat Gul/dpa/AP/picture alliance

Wani rukuni na mata a Afghanistan ya yi wa 'yan Taliban masu mulki da kasar zanga-zanga a wannan Talata. Matan da yawansu bai wuce 30 ba sun taru ne suna zargin Taliban da kisan tsaffin sojojin da suka yi aiki a karkashin gwamnatin da Taliban ta ruguza a watan Agustar da ya gabata. Duk da rashin yawansu, matan sun taru a kusa da wani masallaci a birnin Kabul suna jefa wa gwamnatin Taliban ''bakaken maganganu'' a game da yadda ake kashe jami'an tsohuwar gwamnati a asirce. Lela Basam na cikin wadannan mata.

''Muna son duniya ta ja wa 'yan Taliban kunne su daina aikata laifukan da suke yi. Jami'an tsohuwar gwamnati na cikin babbar barazana. Wannan ya saba da afuwa da alkawuran da Taliban take cewa ta yi wa wadannan jami'ai.'' inji Lela

Daga baya dai rahotanni sun ce sojojin Taliban sun tarwatsa zanga-zangar da matan suka yi. Kazalika sun kwace wa 'yan jarida nau'rorin daukar hoto, daga bisani kuma suka mayar musu na'urorin bayan da suka goge hotunan zanga-zangar da manema labaran suka dauka.