1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Takunkumin Amurka kan cin zarafi a Sudan

Suleiman Babayo MAB
November 12, 2024

Amurka ta saka tunkumi kan daya daga cikin jagororin kungiyar RSF mai fafata yaki a kasar Sudan wanda ake zargin da cin zarafin fararen hula a rikicin.

https://p.dw.com/p/4mwFW
Sudan Darfur El Fasher
Yankin Darfur El Fasher na SudanHoto: AFP

Kasar Amurka ta dankara takunkumin karya tattalin arziki kan daya daga jagororin rundunar mayar da martani na Sudan, Abdel Rahman Joma'a Barakallah bisa zargin cin zarafin dan Adam a lardin yammacin Darfur sakamakon yakin da ke faruwa a kasar. Ma'aikatar kudi ta Amurka ta sanar da haka, inda ta ce jami'in ya yi kaurin suna wajen aikata laifuka kan fararen hula.

Karin Bayani: Sudan: Gwamnati na zargin kasashe makobta da agaza wa 'yan tawaye

Tun watan Afrilun shekarar da ta gabata ta 2023 yaki ya barke tsakanin dakarun gwamnati karkashin shugaban kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma mayakan rundunar mayar da martani ta RSF karkashin jagorancin Janar Mohamed Hamdan Dagalo tsohon mataimakin shugaban kasar. Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kiyasin cewa mayakan rundunar ta RSF da goyoyn bayan tsagerun Larabawa sun halaka fararen hula kimanin dubu-10 zuwa dubu-15 a yankin yammacin Darfur kadai.