Tattalin arziki
Jamus ta nemi ganin mafita tsakanin Amirka da China
June 28, 2019Talla
Batun harkokin kasuwanci na ci gaba da samun tagomashi a taron manyan kasashe da ke sahun gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya na G20 da ke gudana a kasar Japan. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana fata za a samun mafita kan kiki-kaka tsakanin kasashen Amirka da China wadanda suke gaban gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya. Yayin da ake shirin ganawa tsakanin Shugaba Donald Trump na Amirka da takwaransa Xi Jinping na China a gefen taron.
Haka kungiyar kasashen Tarayyar Turai suna tattauna samun kasuwanci ba shinge da kasashen kudancin Amirka. Ana samun dari-dari a kasuwar hannun jari a duniya saboda rashin tabbas na abubuwa da za a cimma a wannan taro na G20 da ke gudana a kasar Japan.