Takarar shugaba Jonathan na Najeriya a zabukan 2015
November 8, 2013A wani abun dake zaman kama hanyar zuwa ga bushewar bakin alkalami ga batu na makomar takara ta shugaban tarayar Najeriya, fadar gwamnatin kasar tace shugaban yana fuskantar kari na matsin lamba domin fitowa dama tsayawa takara a zaben shugaban kasar na shekaru biyu masu zuwa.
An dai kai ga yamutsa gashin baki, an kuma yi batu na alkawari. To sai dai kuma ana shirin karewa tare da jami'yyar PDP mai mulki sake tsaida shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, domin taka rawa a zabukan shekara ta 2015.
Matsin lamba ne hujjar takarar Jonathan
Duk da cewar dai a baya shugaban ya ce sai ta kai shi har ga shekara ta badi kafin fitowa domin bayyana ra'ayinsa kan batun na sake tsayawa domin neman mulkin kasar ta Najeriya, babban mashawarcinsa kan batu na siyasa dai, ya ce shugaban kasar na fuskantar kari na matsin lamba domin sake takara a zabukan na gaba.
Akalla kungiyoyin sa kai 1665 ne dai a cewar Ahmed Gulak yanzu haka ke gwagwarmayar neman tabbatar da tsaida shugaban da takarar tasa tai nisa wajen raba kan 'ya'yan jam'iyyarsa ta PDP, banda kuma kungiyoyin 'yan kasar da ke wajen Najeriyar da su ma ke zake wajen tabbatar da kallon ranar sake takarar ta shugaban kasa.
Duk da cewar dai shugaban kasar zai hakura har ya zuwa ga shekarar mai kamawa domin aman 'yan hanjin da ke cikin ciki, sabon matsayin a fadar Garba Umar kari da ke sharhi kan siyasar ta Najeriya, na zaman kokari na shimfida ga shugaba Jonathan na fara ginin sabon burin nasa.
Tarnaki ga takarar shugaba Jonathan
Koma ya zuwa yaushe ne ake sa ran karatun na Jonathan da kujerar mulki zai zo kuri dai, sabon matsayin na kuma tabbatar da tsoro na kungiyar 'yan bakwai na gwamnonin jam'iyyar da suka share tsawon lokaci suna tawayen abun da suka kira saba alkawarin da ke tsakanin bangaren arewacin kasar da shugaba Jonathan.
Alkawarin kuma a cewar Abdullahi Jalo da ke zaman mataimakin kakakin jam'iyyar PDP na kasa, bai wuce mafarki irin na 'yan tawayen gwamnonin ba.
Tabbatar da alkawari a rubuce ko kuma batu na siyasar bangare dama addini dai, ko bayan rikicin na arewa wani batun da ke zaman tarnaki a tunanin masu adawar dai, na zaman na kundin tsarin mulkin kasar ta Najeriya da ya tanadi wa'adin mulki biyu na shekaru hur-hudu sau biyu. Abun kuma da a cewar Dr Umar Ardo na jam'iyyar PDP ke zaman shingen da ke shirin shiga tsakanin shugaban da burin nasa.
Abun jira a gani dai na zaman mafita a gwagwarmayar ikon da ke sauyin salo dama launi, ke kuma kara jefa harkokin Demokaradiyar kasar cikin rudani.
Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh