1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyaran zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Abdoulaye Mamane Amadou
November 27, 2019

Hukumomin Afirka ta Tsakiya sun dauki matakan inganta zabukan kasar na badi wanda ya hada da kafa kwamiti da zai tsara zabe mai tsafta sai dai tuni matakin ya janyo cece-kuce

https://p.dw.com/p/3TouQ
Zentralafrikanische Republik Kommunikationsminister Ange-Maxime Kazagui
Hoto: Hippolyte Marboua

Kwamitin mai mambobi 27 ya kunshi kusoshin gwamnati da shugabannin hukumomi masu zaman kansu da jami'an huldar diflomasiyya da ministoci, babban burinsa shi ne kafa ingantaccen  tsari da zai bada damar zabukan kasar lamin lafiya ba tare da fitina ba. Sai dai tun ba a je ko ina ba kwamitin na shan suka daga bangharori da dama. Ange-Maxime Kazagui ministan sadarwar kasar ne kuma kakakin gwamnatin birnin Bangui

Ban ga dalilin da ke sanya wa jama'a sukar wannan kwamitin ba, tsarin wata fasaha ce ta kawo sauki ga harkokin shirya zabe".

Sai dai wadannan bayyanai na ministan wanda shi ma dan kwamtin ne bai gamsar da sauran jam'iyyun siyasa da kungiyoyin farar hulaba inda suke yiwa kwamitin kallon haramtacce.

André Nalké Dorogo daya daga cikin 'yan adawa na jam'iyyar URCA yace kundin tsarin mulki da kundin zabe ba su halasta girka wani kwamitinba mai kula da zabe ba bayan hukumar zabe mai zaman kanta.

Yace da zarar kaji an ce wai an kafa wani kwamiti mai sa ido kan yadda za a gudanar da zabe, ka san da akwai manufa. Ban ga amfanin wani kwamiti na daban ba, dole ne mu fito mu bayyana shakkunmu da na jama'a kan yadda ake shirin wannan tafiyar a yanzu, Ina tsamanin ba fa'ida ba ce ga masu mulki a yanzu su mamaye wani bangare na aikin hukumar zabe ta ANE kan batun zaben.

Duk da wannan cece-kucen dai har yanzu kwamitin ya cigaba da aiki gadan-gadan a karkashin jagorancin Firaministan Firmin Ngrebada. Za a gudanadar da zagayen farko na zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki  a cikin watan Disamba n  shekarar 2020.