1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Jonathan da Sanusi

January 12, 2014

Tun bayan wasu rahotanni da ke cewa Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi kira ga Gwamnan babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi ya yi murabus, ake ta sa-in-sa a kan batun.

https://p.dw.com/p/1AoiZ
Nigeria Präsident Goodluck Jonathan Beerdigung Autor Chinua Achebe OVERLAY GEEIGNET
Hoto: Pius Utomi ekpei/AFP/Getty Images

A wani abun da ke zaman kokarin kara fadada rikicin tarrayar Najeriya ya zuwa ga tattalin arzikin kasar mai tangal tangal, tuni dai ra'ayi na banbanta tsakanin sassan kasar daban-daban game da makomar Gwamnan babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi

Ba kasafai dai ya kan kai ga boye abun da ke cikin zuciyarsa ba komai daci. Haka ya sha karawa da masu gidansa bisa banbancin ra'ayi da ma kila akida.

To sai dai kuma daga dukkan alamu tana shirin yin tsami a batun dangantaka a tsakanin Gwamnan babban bankin tarrayar Najeriya Sanusi Lamido Sanusi da kuma hugaban kasar da majiyoyi maras tabbas suka ce ya nemi raba shi da kujerarsa ta shugabancin banki mafi tasiri a kasar.

Zargin bacewar makudan kudade

Duk da cewar dai rikicin ya fara fitowa fili sakamakon wata wasikar da a cikinta gwamnan ke zargin babban kamfanin man kasar na NNPC da batar da tsabar kudi har dalar Amurka milliyan kusan dubu 50, an dauki tsawon lokaci ana takun saka a tsakanin fadar shugaban kasar dake kallon Sanusin a matsayin gwamna mafi taurin kai a cikin tarihin bankin na shekaru kusan 55, ga mutumin da ya rika fitowa yana dagun kara ga halin almubazzarancin mahukuntan kasar na lokaci mai tsawo.

Nigeria Gouverneuer der Zentralbank Sanusi Lamido Sanusi mit Christine Lagarde
Gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi da shugabar Asusun IMF Christine LagardeHoto: Getty Images

To sai dai kuma fitar wasikar da ta zo dai-dai lokacin da fagen siyasar kasar ke kara dumi dai ta harzuka 'yan fadar da suka dauki tsawon lokaci suna wankin kai kamun daga baya su juyo domin huce takaicinsu a kan gwamnan.

Shakku game da bukatar ajiye aiki

Har ya zuwa ranar Juma'a dai babu wani tabbaci a bangaren fadar gwamnatin kasar game da sahihancin bukatar neman ajiye aikin gwamnan tun kafin wa'adin aikin sa a farkon watan Yuni mai zuwa. To sai dai kuma tuni daukacin kasar ta dauki dumi sannan kuma ta ce ahir ga shugaban kasar da babbar jam'iyyar adawar kasar ta APC ta zarga da kokarin wuce gona da iri a fadar Aminu Bello Masari dake zaman mataimakin shugaban jami'iyyar na kasa da kuma ya ce dole ne a kyale gwamnan kammala wa'adin nasa ko da mai zai faru.

"Siyasa da kujerar gwamna ko kuma kokari na zarce makadi cikin rawa, Sanusi dai ya kafa tarihin juya tsarin kudin kasar daga mai tangal tangal ya zuwa daya daga cikin mafiya karfi a daukacin nahiyar Afirka baki daya. Abun kuma da ya kaishi a karo na uku cikin shekaru biyar zamowa shugaban babban banki mafi hazaka a daukacin kasashen nahiyar ta Afirka."

Zentralbank von Nigeria
Shelkwatar babban bankin Najeriya a Abuja

Wannan rikici dai na iya sake maida tsarin komawa gidan jiya in da ake yi wa kasar kallon wata matattara ta 'yan damfara masu neman dama. Abun kuma a fadar Usman Balkore, masanin tattalin arzikin kasar, ke zaman babban hatsari ga masu mulkin na Abuja.

Kokarin ta jin bakin ministan kudin game da tasirin rikicin ga tattalin arzikin kasar ta Najeriya dai ya ci-tura bayan da ta ce ta zo fadar shugaban kasar domin tattauna batun nasarar bashin kasar ta Najeriya.

Da aka tambaye ta ko akwai bukatar ajiye aikin gwamnan babban bankin kasar daga fadar shugaban kasa, sai ta ce "mun zo ne domin tattauna batu mai sanya farin ciki da ya faru ga tattalin arzikin kasar inda abokanmu suka shaida mana muna da offishin kula da basuka mafi inganci a daukacin nahiyar Afirka."

Abun jira a gani dai na zaman mafita a kokarin banbance tsakanin rikicin tattalin arziki da siyasa ga Najeriyar da sannu a hankali al'amura ke kara rikicewa a ciki.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal