1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Jonathan da Sanatoci

April 3, 2014

Hakan ya shafi yunkurin bai wa shugaban Najeriyar ikon gabatar da sauyi ga tsarin mulki, kan cewar hurumin 'yan majalisar ake neman karbewa ta bayan fage.

https://p.dw.com/p/1Bbd8
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Wannan yunkuri dai ya sake taso da kallon hadarin kajin da aka dade ana yi a tskanin bangaren zartaswa da na majalisar, domin kuwa jim kadan bayan da mataimakin shugaban majalisar dattawan Sanata Ike Ekweremandu ya gabatar da kudurin, hatsayi ta taso a majalisar, domin wasu na kallon lamarin a matsayin yunkuri ne na wayon karbe masu ayyukansu.

Lamarin da ya sanya wasu ‘yan majalisar tsalle gefe guda suka ce ba su amince ba, domin kuwa a cewarsu yunkuri ne da zai bai wa shugaban kasar kafar cusa batutuwan da za'a cimmawa a taron kasa da ake gudanarwa cikin tsarin mulkin Najeriyar ta bayan fage. Sanata Babbayo Garba Gamawa ya ce ba wai adawa ba ce, sai dai bukatar sanin abin da tsarin mulki ya tanadar.

"Babu inda aka taba cewa shugaban kasa ya samu dama wajen yin doka domin shi gyara tsarin mulki wani sashi ne na yin doka, shi kansa kundin tsarin mulki majalisa ita keda hurumi na gyaransa, sannan kuma ana zuwa mazabu a ji ra'ayoyin mutane kamar yadda muka yi a baya. Don haka in aka ce shugaban kasa ya fara barin aikinsa na zartaswa, na nada ministoci ko kula da aikin kamar na asibiti a wuri kaza, to ya fara shigowa aikin majalisa a kan kuma ya tsallake, kuma ita majalisar nan ta wuce haka".

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/AP Photo

Wannan takaddama da ta kama hanyar sake jefa aikin gyaran tsarin mulkin Najeriyar yiwuwar fuskantar jinkiri, baya ga jan kafar da aka dade ana fuskanta da ma rashin daidaituwa a tsakanin majalisun biyu na Tarayyar Najeriyar. Aikin da ke neman yi wa majalisar dare. Sanata Kabiru Garba Marafa na mai cewa akwai fa bukatar yin taka tsan-tsan.

"Sai mun yi a hankali wajen gyaran dokoki ko kawo sabbi domin yanzu ka je ka wo wata majalisa ka tsintsinto wasu mutane ka ce su je su zauna su yi wani abu, yanzu kuma kana son abin da suka yi ka dauko shi ka shigo dashi ta bayan gida, to amma tun da baka da hurumi to bari ka yi amfani da majalisar ta kashe kanta da kanta. To idanmu fa a bude yake in gyaran tsarin mulki za'a yi zamu gyara dukkanmu nan ‘yan Najeriya ne."

To sai dai ga Dr Ibrahim Baba kwararre a harakar dimukurdiyyar Najeriya na ganin akwai rashin fahimtar lamarin daga 'yan majalisar a game da batun baiwa shugaban Najeriyar iko gabatar da gyaran tsarin mulki a majalisar. Ya kamata in zai yi shi ba tare da son kai ba babu laifi, ba wata kumbiya-kumbiya in zai yi domin al'umma jama'a ta amfana to ba laifi.

Karte Nigeria

"Na san shugaban kasa shine shi kadai mazabarsa take Najeriya ce gaba daya, don haka wannan abu shi shugaban kasa ya kamata ya tabbatar da zaman lafiya ta hanyar gyaran tsarin mulki, amma fa sai ya hada kai da 'yan majalisa."

Koda ya ke wasu ‘yan majalisar na yi wa wannan yunkuri kallon wata dabara ce ta shirya yadda za'a cusa batutuwan da taron kasar zai cimmawa a tsarin mulkin Najeriyar, to sai dai tun da farko shugaban kasar karara a fili ya bayyana cewa majalisar ce fa keda hurumin amincewa da dukkanin shawrwarin da za'a cimawa kafin su sami shiga cikin tsarin mulkin kasar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar