Aljeriya: Adawa da takarar Bouteflika
March 4, 2019Shugaban na Aljeriya dan shekaru 81 da haihuwa, yana fama da cutar shanyewar jiki tun kusan shekaru shidan da suka gabata, wakilinsa kuma sabon shugaban yakin neman zabensa, Abdulgani Za'alan wanda a madadinsa ya gabatar da takaddunsa na neman tsayawa takara a ofishin hukumar zabe, ya karantawa 'yan kasar jawabin Shugaban da ke cewa..
"Na dauki alkawari gaban Allah da gabanku ya ku 'yan Aljeriya cewa, da zarar kun sake zaba na a karo na biyar, cikin tsukin shekara guda, zan shirya taron kasa da zai tsara sabon kundin tsarin mulki, kana zan gudanar da zaben gaggawa na shugaban kasa wanda ni bazan tsaya takara cikinsa ba. Na yi ammanar cewa, yin hakan, zai kai ga cimma muradunku na kawo sauyi a kasar nan cikin lumana.''
Tuni galibin 'yan takarar shugabancin kasar, wadanda a jiyan suka janye takarar tasu ,da shuwagabannin jam'iyyun adawa suka yi kira ga 'yan kasar da su ci gaba da yin zanga-zanga, domin a cewarsu, ga dukkan alamu, akwatin zabe a kasar bai da wani amfani. Ga alama irin wannan kiran ya samu karbuwa, ganin tun a daren jiya Lahadi fadar mulkin kasar Aljaz ta yi cikar kwari da masu zanga zanga.
A jiya Lahadin ne, wa'adin mika takaddun takarar shugabancin kasar ke karewa, kuma kundin tsarin mulkin kasar ya fayyace cewa, dole ne dan takara ya mika takaddunsa da kansa ba ta hanyar wakilci ba, lamarin da ya sanya masharhanta ke nuna fargabar cewa, zai yi wuya, kan dai ba'a murde wuyan doka za ayi ba, hukumar zaben ta bai wa Bouteflika shedar cancantar tsayawa takara, bayan ta yi nazarin takaddunsa nan da kwanaki goma, kamar yadda dokar zaban kasar ta tsara.