1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar: Taimakon masu mulki

Gazali Abdou Tasawa AH/SB
November 1, 2023

Martani kan matakin kungiyar Tarayyar Afirka na amincewa da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Jamhuriyar Nijar da ma gabatar da jadawali na dafa wa hukumomin mulkin sojan kasar kan komawa tafarkin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/4YHlm
Jamhuriyar Nijar | Masu zanga-zanga
Masu zanga-zanga a Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

A Jamhuriyar Nijar 'yan siyasa da kungiyoyin gwagwarmaya sun soma mayar da martani kan matakin kungiyar Tarayyar Afirka na amincewa da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar da ma gabatar da jadawali na dafa wa hukumomin mulkin sojan kasar a tafiyar mulkin rikon kwarya dan mayar da kasar kan turbar dimukaradiyya. Kungiyar ta AU ta dauki wannan mataki ne a lokacin da kungiyar ECOWAS da hukumomin mulkin sojan Nijar suka kwashe watanni suna zaman 'yan marina a lokacin da mutanen kasar ke shan radadin takunkumin tattalin arziki da aka kargama wa kasar.

Karin Bayani: Matsalolin tsaro bayan juyin mulki a Nijar

Masu zanga-zanga a Jamhuriyar Nijar da ke goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki
Masu zanga-zanga a Jamhuriyar NijarHoto: Djibo Issifou/dpa/picture alliance

Bayan wani zama ne da kwamitin sulhu na kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kan batun rikicin siyasar kasar ta Nijar ta bayyana amincewarta da abkuwar juyin mulki a Nijar tare da bai wa kungiyar ta Tarayyar Afirka shawarar gaggauta nada wakili na musamman na kungiyar wanda zai taya tafiyar mulkin rikon kwarya ta hanyar shirya babban taron kasa da zai mayar da kasar kan turbar dimukaradiyya. Kazalika kwamitin sulhu ya gargadi kungiyar ECOWAS da hukumomin mulkin sojan Nijar ga tunkarar juna domin tattauna hanyoyin warware rikicin kasar ta hanyar lumana da daukar matakan rage radadin takunkumi ga talakawan kasar.

Kungiyar ta Tarayyar Afirka ba ta yi batun maido da hambararren shugaban kasa kujerarsa ta mulki ba. Illa dai kawai ta yi kira da a sake shi shi da iyalansa da duk 'yan siyasar da ke tsare. Kwamitin sulhun kungiyar ta AU ya sanar kuma da shirin aiko da tawaga a Nijar domin tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar kasar domin tsaida jadawalin mayar da kasar kan tafarkin dimukaradiyya. Wanda ke nuni da cewa sannu a hankali kasar ta Nijar ta fara fita daga tarnakin da kungiyoyin kasa da kasa da wasu manyan kasashen duniya suka saka kasar ciki a sakamakon juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yulin 2023.