Bala'iNa duniya
Taimakon kasasshen da suka fuskanci bala'i
August 30, 2024Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana sakin kudi kimanin dalar Amirka milyan 100 domin taimakon aikin agaji a wuraren da ake rikice-rikice na nahaiyar Afirka da nahiyar Amirka gami da nahiyar Asiya da Gabas ta Tsakiya. Za a kashe kimanin kashi daya bisa uku na kudin zuwa kasashen Yemen da za ta samu kamanin dala milyan 20 da Habasha wadda za ta samu kimanin dala milyan 15, wuraren da mutane suka tagayyara sakamakon yunwa.
Sauran kasashen da za su samu wannan tallafi na Majalisar Dinkin Duniya sun hada da Myanmar da Mali da Burkina Faso, da Haiti da Kamaru gami da Mozambik. Su ma kasashen Burundi da Malawi da suka fuskanci guguwa mai dauke da ruwan sama za su samu wannan kudin taimakon jinkan.