Tahirin zababben shugaban Najeriya
April 8, 2015Janar Buhari ya zama shugaban kasa a zamanin mulkin soji daga ranar 31, ga watan Disambar 1983, zuwa 27th ga watan Agustar 1985, inda a wancan lokaci ne Buhari ya kafa asusun nan na rarar mai da jama'a ke alfahari kai.
Domin kudirin samun daidaito cikin lamurar kasa nema ya sanya Janar Buhari neman shugabancin kasar a fagen mulkin demukurdiyya har sau uku, inda ya nemi shugabancin a shekarun 2003, da 2007, da kuma 2011, to amma Allah bai sa y ayi nasara ba. To sai dai a watan Disambar 2014, Janar Buhari ya sami tikitin neman shugabancin kasar karo na 4, a tutar jam'iyyar APC.
To sai da kuma Janar Buhari ya ce shi ba kudi ne da shi ba, domin haka nema bashi da karfin aljihun da zai gudanar da kamfe na neman shugabancin kasa, dalili ke nan ma ya bude asusun da yan Najeriya ne su kansu ke yin karo-karo.
Janar Buhari ya kafa tarihi a Najeriya inda ya zama dan adawa na farko da ya kayar da jam'iyyar mai mulki, wajen lashe zaben ranar 28 ga watan Maris, inda ya kayar da Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP. Buhari yana da mata da yara 9.