Ba ta kashin sojoji da 'yan ta'adda
December 24, 2021Talla
Rundunar ta bayyana ba ta kashin a matsayin wanda suka yi nasara, ganin cewa sun halaka 'yan ta'addan har 22, koda yake suma a nasu bangaren suka yi asarar sojoji sida. Rundunar sojojin sama ta hadaka tsakanin Najeriya da Nijar ne dai suka fafata da 'yan ta'adda, sai sun ce sun samu daga kawayensu na Amirka. Da ma dai yankin na Tafkin Chadi da ke kan iyakokin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, na fama da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram masu gwagwarmaya da makamai da suka addabi kasashen yankin baki daya.