Barazanar kafewa ga tafkin Chadi
October 14, 2015Ya zuwa lokacin da shugabannin kasashen tafkin na Chadi suka zartar da shawarar kafa hukuma ta gudanarwa ga tafkin a shekarar 1964 dai, fadin tafkin ya kai muraba'in Kilomita 25,000 a cikin kasashen na kamaru da Chadi da Najeriya da kuma jamhuriyar Nijer.
To sai dai kuma ya zuwa shekarar bara tafkin ya koma abun da bai wuci murabba'in Kilomita 1,500 ko kuma kaso 10 cikin dari na tsohon adadin. Ana kuma kallon barazanar kafewar tafkin gaba daya nan da wasu shekaru 20 da ke tafe in har masu ruwa da tsaki da shugabancin yankin ba su kai ga daukar matakai kwarara a cikin gaggawa ba.
Barazana ga makoma
Wani binciken kwakwaf kan tafkin da kasar Jamus da hadin kan tarrayar Turai suka dauki nauyi dai ya ce gaggawar na zaman wajibi da nufin ceto tafkin da ma miliyoyin al'ummar da ke dogaro da shi domin harkoki na rayuwa.
Mista Samuel Ukura dai na zaman babban mai binciken kudi na tarrayar Najeriya, daya kuma a cikin jerin jami'an kasashen da suka kaddamar da binciken da ke tada hankali ga sarakuna da ma talakawan yankin.
“ Babban sakon binciken tarrayar Najeriya shi ne tafkin Chadi na kafewa a cikin saurin gaske, daga fadin Muraba'in Kilomita 25,000 a shekarar 1963 ya zuwa kilomita 1,500 a halin yanzu. Dole ne mu ceto tafkin Chad daga bata”.
Ana dai ta'allaka matsalar rashin tsaron da ta yi aure ta kama hanyar tarewa a cikin yankin da gazawar tafkin na biyan bukatar Miliyoyin al'ummar da ko dai ke da sana'ar noma ko kuma ke zaman masuntan gado.
Tattalin muhalli
Abun kuma da a cewar Michael Zenner da ke zaman jakadan Jamus a tarrayar Najeriya ya sanya kai daukin zama na wajibi da nufin ceton yankin baki daya.
“ Yana da muhimmanci yankin tafkin Chadi ya sake zamowa yankin da al'ummarsa za su sake rayuwa da fata na ci-gaba da kuma kula da muhalli a cikinsa. Ina jin kuma ya na da muhimmanci da wannan rahoton masu bincike ke mai da hankali ga batun na muhalli da kuma yadda za'a warware matsalarsa”.
Daya a cikin dabarun tunkarar matsalar dai na zaman janyo ruwa daga kogin Ubangi da ke jamhuriyar Kongo domin tsiyaye shi cikin tafkin Chadi, aikin kuma da kwarraru suka tsara zai lamushe dalar Amirka miliyan dubu 14.5, ko kuma biyu cikin uku na daukacin kasafin kudin tarrayar Najeriya na shekara guda.
Barrister Ahmed Muhammed Abubakar dai na zaman gwamnan Bauchi daya kuma daga cikin gwamnonin da suka saurari rahoton da ke da tasiri kan al'ummarsu. Kuma a ganinsa ana iya samo hanyar fitar da wanda ta tsakar ka akan batun. To sai dai kuma ko bayan batun taimako na waje a fadar Engineer Sanusi Imran Abdullahi da ke zaman sakatern da ke kula da tafkin yanzu, akwai dabaru a kasa da ke iya sake tabbatar da farfado da tafklin domin amfanin kowa.