1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin kare hakkin dan Adam a Afirka

February 22, 2017

Rahoton kungiyar Amnesty International na shekara-shekara ya nuna wasu kasashen Afirka da ke fama da rikice-rikice ciki har da Sudan da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango an fuskantar take hakkin dan Adam.

https://p.dw.com/p/2Y316
Deutschland PK Amnesty International Report 2016/2017
Hoto: DW/N. Jolkver

Sudan da Sudan ta Kudu sun kasance a sahun gaba na kasashen da Amnesty ta nunar da cewar tauyen hakkin bil Adama na neman zama ruwan dare a cikinsu. A jimlance dai kasashe 10 na Afirka ne suka kasance a rukunin kasashe 159 na duniya da Amnesty ta yi tsokaci a kansu. Ita kungiyar da ke da mazauninta a birnin London ta nunar da cewar bisa ga dukanin alamu, hukumomin Sudan sun yi amfani da makami mai guba a yankin Darfur. Yayin da a Sudan ta Kudu kuwa, fararen hula sun ci gaba da kasancewa cikinhalin nin 'yasu sakamakon tauye dokokin kasa da kasa tsakanin bangarorin da ke fada da juna. Stephen Cockburn jami'in Amnesty da ke kula da tsakiya da kuma yamamcin Afirka ya ce musaganwa 'yan adawa na neman zama ruwan dare a wadannan kasashe.

"A kasashen Cote d 'ivoire da Chadi da Gabon da kongo, gwamnati na shafa wa 'yan adawa kashin kaji tare da far wa masu zanga-zanga. Akwai shaidu da ke nuna cewar a duk lokacin da takakawa ko yan siyasa suka tayar da kayar baya ana kashesu. Ko a Najeriya sai da masu neman ballewa suka dandana kudarsu a hannun jami'an tsrao. Haka lamarin ya kasance a Kamaru da Gambiya da Guinea gami da Saliyo."

Bürgekrieg in Elfenbeinküste in 2011
Hoto: dapd

Kungiyar da ta himmatu wajen kare hakkin bil Adama a duniya ta nunar da cewar gwamnatin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango ta tsare masu fafutukar tabbatar da mulkin dimukaradiyyar ba tare da kwakkwaran dalili ba. Buga da kari ma dai wasu daga cikinsu sun shafe tsawon lokaci a gidany ari ba tare da gurfana gaban kuliya ba. Sai dai kuma rahoton Amnesty bai tabo batun amfani da karfi da jami'an tsaron kamaru da kan 'an kasar da ke amfani da Ingilishi ba bayan da suka kosa da neman mayar da su saniyar ware da ake yi. Stephen Cockburn ya ce sun saba tsokaci kan wannan batu.

Brasilien Protesten gegen Begrenzung der Staatsausgaben
Hoto: picture-alliance /dpa/J. Alves

"Mun soki amfani da karfi fiye da kima da jami'an tsaro suka yi a lokacin da suka bude wuta a kan masu zanga-zanga. Sannan mun nuna rashin dacewa da katse kafar sadarwa ta Internet da aka yi a yankin da ke magana da Ingilishi. Kana mun nuna rashin dacewa da kame shugabannin kungiyoyin fararen hula da aka yi."

Sauran kasashe da Amnesty ta ce sun yi kaurin suna a fannin take hakkin dan Adama a Afirka, sun hada da Angola da Botswana da Lesotho da Mozambik da Swaziland.