SiyasaAfirka
Taba Ka Lashe: 15.11.2023
November 28, 2023Talla
Akwai darurruwan dalibai Hausawa da ke zaune a kasar Morocco su na yin karatu a makarantu da birane dabam-dabam. Yawancinsu sun je kasar Moroko ne daga kasashen Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da kasar Ghana suna neman ilimi. Sai dai sun samu sabuwar rayuwa a kasar ta Maroko saboda sauyin al'adu da yanayin abinci.