Sweden ta zama memba na 32 na kungiyar NATO a hukumance
March 7, 2024A yayin wani bikin mika mata wasu takardu da aka gudanar a birnin Washington ne kasar Sweden ta zama memba ta 32 a kungiyar tsaro ta NATO a hukumance. Wannan kasa ta yankin Scandinavian da ta zabi shiga cikin kawancen ne bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, lamarin da ya kawo karshen shekaru 200 da ta shafe a matsayin 'yar ba ruwanmu.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi amfani da wannan dama wajen yin tsokaci kan dogon zaman jiran tsarin amincewa, inda ya ce wannan samun kujera da Sweden ta yi a kungiyar NATO ya nuna raunin da manufofin Rasha ke da shi. A nasa bangaren, firayiministansa Sweden Ulf Kristersson ya danganta matakin da nasara ta 'yanci.
Shekaru biyu Sweden ta shafe tana kokarin shiga kungiyar tsaro ta NATO kafin hakarta ta cimma ruwa.