Suu Kyi ta yi jawabin godiya a birnin Oslo
June 16, 2012A wannan Asabar a birnin Oslo na ƙasar Norway shugabar adawa ta kasar Burma, Aung San Suu Kyi ta yi jawabinta na godiya bisa karrama ta da aka yi da kyautar zaman lafiya ta Nobel shekaru 20 da suka gabata. A cikin jawabin da ta yi a wani zaure da ya yi makil da jama'a Suu Kyi mai shekaru 66 ta ce za ta ci gaba da gwarwarmaya har sai ta aiwatar da cikakken 'yanci na siyasa a ƙasarta. Ta ce har yanzu akwai firsinonin siyasa da ke daure. Wannan ziyara da Suu Kyi ke yi a birnin Oslo na zaman irinta ta farko da ta kawo nahiyar Turai cikin shekaru 24 da suka gabata.
A shekarar 1991 ne aka karrama Suu Kyi da wannan kyauta bisa gwargwarmayar da take yi domin kwatar 'yanci da kuma aza ƙasar akan turbar demokuraɗiyya. To amma danta ne ya amshi kyautar a madadinta kasancewar tana a karkashin daurin talata a wancan lokaci. A dai halin yanzu sojojin ƙasar ta Burma sun miƙa mulki ga gwamnatin farar hula, kuma sannu da hankali ana samun sauyi na siyasa. A shekarar 2010 ne aka saki Suu Kyi daga daurin talalar da ake mata, kuma yanzu haka tana da kujera a majalisar dokokin ƙasar.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal