1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta na tangal-tangal a Khartoum da Darfur.

Mahmud Yaya Azare
April 28, 2023

A daidai lokacin da ake ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Khartoum, fada ya barke a yankin Darfur da ke yammacin Sudan, yankin da ya jima yana fuskantar rikicin kabilanci.

https://p.dw.com/p/4Qh9Q
Sudan | Kämpfe in Bahri / Khartum
Hoto: social media video via REUTERS

Duk da fara aiki da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku da kungiyar IGAD, ta kasashen gabashin Afirka ta gabatar, fada ya ci gaba da kaurewa tsakanin bangarori biyu da basa ga maciji da juna a birnin Khartoum da dubun dubatan mutane ke ci gaba da ficewa daga cikinsa don tsira da rayuwarsu. Sai dai rahotanni na cewa har yanzu ana yi wa dubban fararen hula kofar rago:

Hakan dai na zuwa ne adaidai lokacin da mummunan yaki tsakanin bangarorin biyu ya barke a yankin Darfur, wanda dama can karfin jami'an tsaron da aka baza a yankin ne ya tilasta wa kabilu masu gwabza fada da juna mika wuya, lamarin da ya sanya ake nuna fargabar sake barkewar fadar kabilanci da zai iya jefa kasar cikin yakin basasa.

Sudan - Mata da yara a Darfur
Sudan - Mata da yara a Darfur Hoto: picture-alliance/AP Photo/K. Prinsloo

Kamar dai yadda rundunar sojin gwamnati ke cewa, ta kaddamar da farmaki a yankin Darfur da ke zama tungar mayakan yan tawayen RSF,don dakile kwararar makamai da mayaka daga yankin zuwa birnin Khartoum.

A farkon wannan rikicin dai, kungiyoyin mayakan sa kai da dama da ke yankin na Darfur sun fito sun nuna cewa basa goyan bayan kowane bangare da ke gwabza yakin kwadayin mulki.

To sai dai kamar yadda Salah Khaleel mai fashin baki a cibiyar binciken Al-ahram da ke Masar ke cewa rikicin Darfur bai rasa nasaba da raunin da gwamnatin Khartoum ta yi:

Sudan | Ta'adin yaki a Khartoum
Sudan | Ta'adin yaki a KhartoumHoto: Marwan Ali/Ap Photo/picture alliance

"A duk lokacin da aka samu rauni a cibiyar gwamnati to kananan kungiyoyin sa kai da mabarnata kan ci karensu babu babbaka. Don haka a ganina, muddin ba a gaggauta magance wannan yakin ba, za a dinga samun bullar fadace fadace a ko ina a Sudan, bana kabilanci kadai ba, harma da ayyukan tarzomar yan fashi da ayyukan ta'adanci da kungiyoyi masu matsanancin ra'ayin Islama."

 A hannu guda, tuni wasu tsofin kungiyoyin mayakan sa kai a kasar, suka bayyana aniyarsu ta kafa rundunar raba gardama da za ta shiga tsakanin janar-janar din biyu ta hanyar anfani da tsinin bindiga don dakatar da abin da suka kira kokarin wargaza Sudan,l amarin da masharhanta ke gani zai kara sarkakiyar rikicin.