1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin murnar bukukuwan Kirsimeti

Abdoulaye Mamane Amadou
December 24, 2019

Shugaban tarayyar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya mika sakon taya murna ga al'ummar kasar a albarkacin bukuwan Kirsimeti tare da kira ga jama'a da su jajirce.

https://p.dw.com/p/3VI12
!!! SPERRFRIST BEACHTEN !!! - Berlin | Fototermin zur Weihnachtsansprache des Bundespräsidenten Frank-Walter Steinmeier
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Shugaba Frank-Walter Steinmeier, ya yi kira ga jama'a da su kara karfafa tafarkin dimukuradiyya da taimaka wa juna a cikin yanayi na hulda mafificiya, a yayin jawabinsa na sakon taya murna zuwa ga al'ummar kasar kan bukukuwan Kirsimeti. Shugaban ya kara da cewa bayan harin da ya auku a wata majami'ar Yahudawa da ke Halle, lokaci yanzu na kara hadakanmu ba tare da wani bambanci ba a tsakaninmu.