1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Spain da Ukraine sun kulla yarjejeniyar tsaro

Abdoulaye Mamane Amadou
May 27, 2024

Kasashen Spian da Ukraine sun kulla yarjejeniyar tsaro da ka iya ba wa Ukraine damar cin moriyar tallafin makaman yaki daga Spain

https://p.dw.com/p/4gKnR
Sarkin Spain Felipe na VI na tarben shugaba Wolodymyr Zelensky
Sarkin Spain Felipe na VI na tarben shugaba Wolodymyr ZelenskyHoto: picture alliance / PPE

Shugaba  Volodymyr Zelensky  na Ukraine ya sauka kai ziyara a birnin Madrid a kasar Spain a kokarinsa na ganawa da mahukuntan kasar don samun tallafin makaman yaki.

Karin bayani : Sabbin hare-haren Rasha a Ukraine sun salwantar da rayuka

Hukumomin Kiev da Madrid sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da ta kai Yuro biliyan daya, da za ta ba wa Ukraine damar cin moriyar tallafin manyan makaman yaki daga Spain a yayin ganawar da Shugaba Zelensky zai yi da takwaransa na gwamnatin Spain Pedro Sánchez a fadar Moncloa.

A makon da ya gaba ne dai Shugaba Sánchez ya lashi takobin kulla yarjejeniyar tsaro da Ukraine da zarar dama ta samu don taimaka mata farfadowa daga mamayar Rasha.

Karin bayani :Rasha ta musanta zargin shirin mamaye yankin Kharkiv na Ukraine

A baya bayan nan dai Shugaba Zelensky, ya kaddamar da rangadin kasashe abokan dasawa da Ukraine a kokarinsa na ganin ya kulla yarjejeniyar tsaro tamkar irin wacce ya yi da kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya.