1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya na fuskantar matsanancin fari

Binta Aliyu Zurmi
December 20, 2021

Akalla mutum daya cikin hudu na fuskantar barazanar yunwa a Somaliya a sabili da fari da kasar ke fuskanta a cewar Majalisar Dinkin Duniya a wani rahoton gargadi da ta fidda a yau.

https://p.dw.com/p/44ZrV
Flash-Galerie Somalia Flüchtlingslager in Mogadishu
Hoto: DW

Wannan dai na zuwa ne bayan karancin ruwan saman da kasar da ke fama da rikicin ta'addanci ta fuskanta na kusan damina hudu a jere. A cewar rahoton matsalar za ta yi kamarin da za ta kai ga barin kusan mutum miliyan 5 ga bukatar agajin gagawa na abinci.

Sama da shekaru 30 Somaliyar bata taba fuskantar irin wannan hali na fari da ta shiga ba. A cewar jami'in hukumar tallafin abinci Adam Abdelmoula, kananan yara daga shekaru biyar zuwa kasa wajen dubu 300 ke cikin hadarin fuskantar karancin abinci mai gina jiki cikin watanni masu gabatowa..

A watan da ya gabata ne mahukunta a Somaliya suka ayyana wannan matsala ta fari a matsayin agaji na gagawa.