Sojojin NATO sun fara ficewa daga Iraki
January 7, 2020Talla
Wata sanarwa da kungiyar NATOn ta fitar na cewa ta dau matakin janye wasu sojojinta daga wasu muhimman wurare ciki da wajen Iraki dan kaucewa samun matsala, amma ta ce tana nan daram a cikin kasar, kuma za ta cigaba da horo idan hali yayi bayan da ta dakatar bayan kishe janar Soleimani a makon jiya.
Kasar Jamus ta janye dakarunta 33 daga Iraki zuwa kasar Jordan, sai dai Faransa ta ce sojojinta za su cigabad a zama cikin kasar Iraki.
Akalla sojojin hadaka 500 da kungiyarNATON ta jiba a Iraki da zimmar horas da sojojin kasar dabarun yaki da mayakan IS, bayan bukatar haka daga gwamnatin Bagadaza a 2018.