1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin gwamnatin Yemen sun kai hari a sansanin masu adawa

September 24, 2011

Dakarun na Yemen sun hallaka akalla masu bore 5 a wani harin da suka fara kaiwa tun daga daren Juma'a

https://p.dw.com/p/12foJ
Masu zanga-zanga suna kare kansu ta mayar da martani da duwatsuHoto: AP

Sojoji a Yemen sun hallaka akalla masu bore biyar a wani samamen da dakarun suka kai a daren Juma'a a babban birnin kasar wato Sana'a. Harin da suka kai a dandalin neman Canji, inda ke zama cibiyar gudanar da ayyukan zanga-zangar ya zo ne bayan dawowar ba zatan da shugaba Ali Abdallah Saleh ya yi daga Saudiyya, inda ya yi watanni ukku yana karbar magunguna, sakamakon raunin da yayi bayan wani harin da masu bore suka kai fadar mulkin sa a ranar 3 ga watan Yunin da ya gabata. Masu gwagwarmayar samar da dauwammaman canji a kasar sun kafa sansani a dandalin na neman Canji tun a watan Janairun wannan shekarar, sadda suka fara neman ganin karshen mulkin na shugaba Saleh.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Halima Balaraba Abbas