Sojoji sun aiwatar da juyin mulki a Masar
July 4, 2013A wani jawabi ta gidan talbijin ranar Laraba da yamma ministan tsaro, kuma babban hafsan hafsoshin Masar, Abdel Fatah al-Sisi, yace an kawar da shugaban ne domin tabbatar da tsaro da kare rayukan jama'a. Sojoin sun kuma tabbatar da cewar Mursi yanzu haka ana tsare dashi a wani sansanin soja a bayan garin birnin Alkahira.
Tun a ranar Litinin ministan tsaro, kuma hafsan hafsoshin sojan Masar, Janar Abdel Fattah al-Sissi yace a bayan tashin hankali da zuba da jini na tsawon mako guda, ya baiwa shugaban na Masar da masu adawa dashi tswon kwanaki biyu domin su sulhunta tsakanin su. Bayan wucewar wannan wa'adi, da kuma rashin nasarar duk wani mataki na neman sulhu, Janar al-Sisi ya baiyana a gidan talbijin, inda ya sanar da cewar sojojin sun kawar da mulkin Mohamed Mursi na tsawon shekara guda, tare kuma da jingine sabon kundin tsarin mulkin da majalisar dokokin kasar da jam'iyar yan uwa musumi ta mamaye ta amince dashi, ya kuma fara aiki a shekarar da ta wuce. Kafofin yada labarai tun a ranar Laraba suka sanar da cewar shi kansa shugaba Mohammd Mursi yana karkashin daurin talala a sani sansani na rundunar tsaron fadar shugaban kasa, yayin da aka bada umurnin kama manyan jami'an jam'iyarsa ta yan uwa musulmi fiye da dari ukku. Bayan zanga-zanga na kwanaki da dama, dubban yan Masar sun biyana jin dadinsu a game da matakin da sojojin suka dauka, inda ma wani dan Masar dake baiyana ra'ayinsa yace:
Ina matukar farin ciki da wannan mataki, kazalika, dukkaninmu, daga dukkain bangarori da muka taru a nan hakan muke ji. Ana iya cewa an yanto kasarmu daga masu mulki mai tsanani. Jam'iyar Yan Uwa Musulmi ta kawo mana matsaloli masu tarin yawa.
Tuna ranar Laraba da rana, dubban mutane suka sake taruwa a dandalin yanci na Tahrir, bisa sauraron irn matakin da sojojin suka shirya dauka. Shi kansa shugaba Mursi a wani jawabi kafin wucewar wa'adin da sojojin suka shimfida, yace bai ga wani dalili na sauka daga mulki ba, kamar yadda duban yan zanga-zangar suka nema, yayin da magoya bayansa suka yi nuni da halaliyar shugabancinsa a matsayin mutumin da yan Masar suka zabe shi, kuma ya kama aiyukan mulki yau shekara guda kenan. Masu lura da al'amuran yau da kulum, sun yi nuni da cewar matakin da sojoin suka dauka na kawar da Mursi daga kan mukaminsa, zai ya jefa kasr cikin wani halina tsaka-mai-wuya. A hannu guda, alhakin sojoji ne su tabbatarda kwanciyar hankali da kare rayukan jama'a, amma a daya hannun, matakin nasu ya kawo karshen mulkin shugaban kasa na halali, wanda aka zabe shi ta hanyar democradiya, karon farkoda aka sami hakan a Masar. Ganin kuma cewar shugaban ba shin da kansa yayi murabus ba, akwai tambayar makomarsa. Dangane da haka, wani mutum a dandalin Tahrir, ya baiyana ra'ayin mafi yawan wadanda suka taru domin zanga-zangar adawa da shugaban.
Yace wajibi ne a jefa shi gidan kaso, kuma tilas ne a gurfanar dashi gaban shari'a. Mutane da yawa sun rasa rayukansu a zamanin mulkinsa, wasu kuma an yi masu kisan gilla, ba kuma zamu manta da wadannan mutane ba.
Sojojin da suka kawar da mulkin Mohammed Mursi, sun gabatar da sunan shugaban kotun kololuwa ta Masar, Adly al-Mansour a matsayin shugaban kasa na wucin gadi, kuma ana sa ran za'a rantsar dashi kan wannan mukami yau. Matakin farko da zai dauka shine kokarin samar da zaan lafiya a kasar, saikuma fara shirye-shiryen zaben sabon shugaban kasa da na yan majalisar dokoki.