1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sojin Isra'ila sun yi wa Zirin Gaza kawanya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 6, 2023

Kwamandan sojin Isra'ila Manjo Janar Yaron Finkelman ya ce gumurzun da suka yi a Talata shi ne mafi zafi tun bayan fara yakin

https://p.dw.com/p/4ZpGT
Dakarun Isra'ila ke sintiri a GazaHoto: Ronen Zvulun/Reuters

Dakarun sojin Isra'ila sun yi wa Kudancin Zirin Gaza kawanya a Larabar nan, inda suke ci gaba da fafatawa da mayakan kungiyar Hamas a kan tituna da sauran gine-ginen da suka buya a ciki, a yakin da yanzu haka ke cika watanni biyu ana gwabzawa.

Karin bayani:Harin Isra'ila a Gaza ya hallaka fitaccen masanin kimiyya Bafalasdine Sufyan Tayeh da iyalansa

A Talatar nan dai an hango tankokin yakin Isra'ila da dakarunta dauke da manyan makamai na kutsawa cikin yankin Khan Yunis da ke Kudancin Zirin Gaza tare da ruwan bama-bamai, inda aka hango yadda fararen hula ke gudun tsira, kamar yadda wani ganau ya shaidawa kamafanin dillancin labaran Faransa AFP.

Karin bayani:Amirka ta bai wa Isra'ila kyautar bama-bamai

Wani kwamandan sojin Isra'ila Manjo Janar Yaron Finkelman, ya ce gumurzun da suka yi a Talata shi ne mafi zafi tun bayan fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.