1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta dace da lambar Nobel ta zaman lafiya

October 14, 2011

A game da nahiyar Afirka, mafi yawan jaridun Jamus a wannan mako sun duba ƙasar Liberiya ne, sai kuma batun tsaro a Somalia da Kamaru inda aka yi zaɓen shugaban ƙasa a ƙarshen mako da ƙasar Sudan.

https://p.dw.com/p/12rrv
Shugabar Liberiya Ellen Johnson SirleafHoto: AP

Mafi yawan jaridun na Jamus a wannan mako mai ƙarewa sun maida hankalin su ne kan Liberiya, inda shugabar ƙasar, Ellen Johnson Sirleaf ta sami lambar Nobel ta zaman lafiya ta wannan shekara, ko da shike 'yan ƙalilan sun duba zaɓen ƙasar Kamaru da halin da ake ciki a Somalia.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta kwatanta shugabar Liberiya, Ellen Johnson Sirleaf a matsayin mace mai kamar maza. Jaridar tace a matsawon mulkin da tayi na shekaru shidda, Sirleaf ta nuna cewar ita ma ba kanwar lasa ba ce tsakanin shugabannin nahiyar Afrika, waɗanda bisa al'ada, yawancin su yan mulkin kama karya ne. Ga shugaban ta Liberia, wannan girmamawa tazo a kan lokacin da ya dace, musamman a kwanakin karshe na kampe na zaben shugaban kasa da aka yi a farkon mako. Jarifar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace dama dai akan ce wai duk wanda yayi da kyau, to kuma zai ga da kyau. Lambar ta Nobel Ellen Johnson Sirleaf ta same ta ne a sakamakon gwagwarmayar tabbatar da kare haki da yancin mata a kasar da nahiyar Afrika baki daya.

Ita ma jaridar Die Tageszeitung ta tabo Liberia, inda tace Mama Elli, kamar yadda mafi yawan yan kasar suke kiran shugabar tasu, tun a kampe na zaben farko da ta shiga ta nuna cewar tana da matukar kwazo, inda ta sami nasara jim kadan bayan mummunan yakin basasa da ya nemi raba kan al'ummar kasar. Tun kafin hakan ta nuna cewar ita ma dai yar gwagwarmaya ce, wanda shine abin da ya kai ta ga matsayin da take a yanzu da kuma samun lambar Nobel ta zaman lafiya a wannan shekara.

A game da halin da ake ciki a Somalia, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ambaci wata sanarwa daga rundunar Amiscom, wato rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen Afrika dake kasar. Rundunar tace wai sojojin ta yanzu haka suna mallakar birnin Mogadishu gaba dayan sa, bayan da suka kwace sauran yankin dake hannun mayakan al-Shabaab. Jaridar tace taji kakakin rundunar Amiscom, Paddy Akunda yana cewa ko da shike dakarun al-Shabaab sun dace yankuna a bayan birnin Mogadishu, amma garin gaba daya an tsabtace shi daga aiyukan wadannan yan tawaye. Sai dai inji jaridar, wannan nasara ce rabi da rabi, domin kuwa Mogadishu, kamar sauran Somalia gaba daya, yana fama da mummunan bala'in fari, da shine mafi tsanani a kasar tsawon fiye da shekaru 60.

Wahl in Kamerun
Shugaban Kamaru Paul BiyaHoto: dapd

Jaridar Süddeutsche Zeitung a sharhin ta, ta tabo zaben da aka gudanar ne a Kamaru a karshen makon jiya, inda tace ko da shike har yanzu ba'a gabatar da sakamakon zaben na shugaban kasa ba, amma shugaba mai ci a yanzu, Paul Biya, wanda shekaru 29 kenan yana kan mulki, a wannan karo ma, babu tantama shine zai lashe shi. Tun kafin a bada sakamakon wannan zabe, jam'iyun adawa, musamman babbar jam'iyar SDF ta dan takara, John Fru Ndi tayi korafin magudi, inda tace tun kafin zaben ma, aka nuna rashin gaskiya ta hanyar tsara kundin rajistar masu zabe yadda zai dace da bukatun gwamnati. Jaridar tayi tambayar dalilin ma da ya sanya har yanzu, mako gudana bayan zaben na shugaban kasa, har yanzu ba'a ga alamar lokacin da za'a fitard a sakamakon sa ba.

A karon garko tun bayan ballewar yankin kudancin Sudan da kuma samun mulkin kansa, shugaban sabuwar yantacciyar kasar, Salva Kiir ya ziyarci takwaran aikin sa na arewaci, Omar Hassan al-Bashir. Dangane da haka, jaridar Neues Deutschland tace wannan ziyara wata alama ce dake nuna cewar shugabannin biyu suna da niyyar daukar matakan warware al'amuran dake ci gaba da raba kan kasashen su, tun da yankin kudancin Sudan ya sami mulkin kansa ranar tara ga watan Yuli. Wadannan al'amura kuwa sun hada har da makomar yankin Abyei mai arzikin man fetur da batun yan gudun hijira da yadda ƙasashen biyu za su rika amfani da ruwan kogin Nil.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita Usman Shehu Usman