1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Koriya za su gana

Abdourahamane Hassane
March 24, 2018

Wakilai na kasashen Koriya ta Arewa da ta Kudu za su gana a makon gobe domin share fage ga wata tattaunawa da za a yi a cikin watan Afrilu tsakanin jagoran Koriya ta Arewa Kim Jong Un da kuma na ta Kudu Moon Jae In.

https://p.dw.com/p/2utvt
Nordkorea Südkorea innerkoreanische Gespräche Moon Jae-in und Kim Jong Un
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Young-Joon

Bangarorin biyu za su tattauna  yadda za a kara samar da masalha tsakanmin kasashen biyu tare da warware rashin zutuwar da ke a tsakaninsu. Wannan dai shi ne karo na uku da shugabannin Koriya ta Arewan da ta Kudu za su gana tun bayan yakin da kasashen biyu suka yi a shekara ta 1950 zuwa 1953.