1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin G7 sun yi kira ga yaki da ta'addanci

Salissou Boukari
May 27, 2017

A taronsu na birnin Taormina na kasar Italiya, shugabannin kungiyar G7 sun yi kira ga masu kula da shafukan Internet da su sa ido kan bayannan farfaganda da masu tsattsauran ra'ayi suke yadawa.

https://p.dw.com/p/2dfVL
G7 Treffen Sizilien Leaders of the G7 pose after signing the 'G7 Taormina Statement on the Fight Against Terrorism and Violent Extremism' at the G7 summit in Taormina
Shugabannin kungiyar G7 a babban zaman taron su na birnin Taormina a kasar ItaliyaHoto: Reuters/Bundesregierung/G. Bergmann

A wannan Asabar din ce shugabannin za su dukufa wajen ganin sun samu daidaito kan batutuwa da suka shafi dumamar yanayi, da kuma kasuwanci na bai daya bayan da suka shafe yinin ranar Juma'a ba tare da shawo kan Shugaba Donald Trump na Amirka ba, kan batun dumamar yanayi, duk kuwa da kokarin da kasashe irin su Faransa, Jamus, Italiya da ma Tarayyar Turai gami da kasashe irin su Japan da Kanada ke yi, na ganin ya canza ra'ayin da yake da shi kan batun.

Da yammacin wannan rana kuma shugabannin na G7 za su gana da shugabannin kasashe biyar da aka gayyato na Afirka da suka hada da Jamhuriyar Nijar, Tarayyar Najeriya, Habasha, Kenya da kuma Tunisiya. Kasar Italiya da ke jagorancin kungiyar ta G7, ta bada babban mahimmanci na hulda da kasashen Afirka, musamman ma kan abun da ya shafi 'yan gudun hijira.