Shugabannin diflomasiyyar Faransa da Jamus na ziyara a Nijar
May 3, 2016Talla
Da safiyar yau din nan dai tawagar ministocin biyu ta gana da shugaban kasa Issoufou Mahamadou, sannan daga bisani ta yi wasu ziyarce-ziyarce a cibiyar yaki da ta'addanci da ke birnin na Yamai, tare da hawa kan ruwan kogin isa domin gane wa idanunsu yadda kogin ke fuskantar koma baya.
A halin yanzu dai tawagar ministocin ta gudanar da wani zaman taro tare da Firaministan na Nijar Briji Rafini, gami da ministocin cikin gida da na harkokin noma da kiwo, sannan daga bisani za su yi wani taron manema labarai kafin sukai wata ziyara a wata cibiyar 'yan gudun hijira da ke karkashin kulawar kungiyar kasa da kasa mai kula da 'yan gudun hijira ta OIM.