Shugabannin Afirka da suka karyata cutar AIDS
Ilimi shi ne ginshikin rayuwa, a bana taken ranar yaki da cutar AIDS ta duniya shi ne ''Ka San Matsayinka". Fadakarwa na taka rawa a yaki da cutar amma wasu shugabannin Afirka sun ki bayar da hadin kai ga fafutukar.
Karyata cutar
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya kafa tarihi bayan da ya karyata binciken masana kan cewa HIV na haifar da AIDS. Ya shawarci jami'an kiwon lafiya da su yi amfani da magungunan gargajiya na ganye don warkar da wadanda suka kamu da cutar. Masana sun nemi a tuhume shi kan laifin keta haddin dan Adam bayan mutuwar mutum dubu 300 da suka bi umarninshi.
Shari'ar Shugaba Jammeh
A shekarar 2007 tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh ya tilasta masu fama da cutar AIDS shan maganin da ya kirkiro da kansa. An gano hade-haden magungunan gargajiya ne da ya hada da ganyeyyak. Mutanen da ba a iya sanin adadinsu ba sun halaka. Jammeh da ke tutiya da baiwa ta dabam ya kasance shugaba na farko da aka soma yi wa shari'a bisa keta haddin masu fama da cutar HIV.
A yi wanka
Tsohon shugaban Afirka ta Kudu da ya ja hankali kuma shi ne Jacob Zuma. Bayan zarginsa da yi wa wata mata mai dauke da cutar fyade a shekarar 2006, Zuma ya ce ba ya fuskantar barazanar kamuwa da cutar don a cewarsa ya sheka wanka bayan saduwar. A shekarar 2010 ya nuna wa duniya sakamakon bincike don tabbatar bai kamu da cutar ba, don nuna adawa da tsangwamar da ake yi wa masu fama da AIDS.
Ban da kwororon roba
Shugaban Yuganda Yoweri Museveni ya dauki dogon lokaci kafin ya shiga yakin da ake da annobar AIDS. A shekarar 2004, a yayin wani taro kan yaki da cutar a kasar Thailand, ya soki matakin yin amfani da kariya na kwororon roba, ya ce yin hakan ya saba wa al'adun Afirka. An dauki kalaman na sa a matsayin wani barkwanci ganin yadda mutane suka bushe da dariya.
Haraji kan AIDS
Wasu matakai na shugabannin Afirka kan yakar AIDS bai zo wa wasu da dadi ba. Tsohon shugaban Zimbabuwe, Robert Mugabe a shekarar 1999 ya sanya a biya wani haraji don tallafa wa marayu da masu fama da cutar, ya fuskanci tirjiya. Duk da haka dokar biyan harajin na nan har yanzu. A shekarar 2004 ya ce cutar ta kama wani daga cikin danginsa inda ya kara da cewa cutar babbar barazana ce ga kasar.
Abin alfahari
Gudun karayar tattalin arziki ya kasance dalilin da kasashen Afirka suka nemi karyata cewa akwai AIDS. Amma tsohon shugaban Zambiya Kenneth Kaunda ya fito ya sanar da yadda cutar ta halaka dansa a shekarar 1987. A shekarar 2002, ya kasance shugaban Afirka na farko da ya amince da yin gwajin cutar a bainar jama'a. Har ya zuwa yanzu ya na ci gaba da fafutukar yaki da cutar AIDS.
Tilasta gwaji
Edgar Lungu ya ci gaba da yaki da cutar AIDS bayan mulkin Kaunda, sai dai ya yi ta cin karo da matsaloli bayan da ya tilasta sai kowane dan kasa ya yi gwajin kwayar cutar. A shekarar 2016 ya ce mutane ba su da zabi face su yi gwajin. Amma jama'a sun ki su amince, dole ya hakura musamman bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce matakin ka iya janyo wa masu fama da cutar tsangwama.